1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 70 na kafa Isra'ila ina makoma?

Ahmed Salisu
April 19, 2018

A wannan Alhamis din ce aka cika shekaru 70 da kafa kasar Isra'ila, lamarin da ya sanya mahukunta da al'ummar kasar gudanar da bukukuwa na murna yayin da Falasdinawa ke juyayi a wannan rana.

https://p.dw.com/p/2wKjo
Israel Jerusalem Feier Unabhängigkeitstag
Hoto: Reuters/R. Zvulun

Kade-kade da wake-wake ne dai suka mamaye bikin na cikar Isra'ila shekaru 70, inda jama'a da dama daga sassan kasar daban-daban suka hadu a dandalin nan na Rothschild Boulevard da ke Tel Aviv inda a nan ne David Ben-Gurion wanda shi ne firaminitsan kasar na farko ya ayyana kafa kasar Isra'ila a ranar 14 ga watan Mayun 1947.

Sai dai ana yin wannan bikin ne cikin watan Afrilu ba Mayu ba duba da irin sabanin da ake da shi tsakanin kalandar Yahudawa da kuma ta Miladiyya.

David Ben Gurion liest die Unabhängigskeits-Erklärung
David Ben Gurion firaministan Isra'ila na farko ke jawabin samun cin gashin kaiHoto: Israeli State Archive

Duk da cewar 'yan Isra'ila na nuna murnarsu da zagayowar wannan rana, wasu 'yan kasar ciki kuwa har da fitattcen dan fim din nan na kasar wato Yair Lehman na nuna damuwa da makomar kasar musamman ma dagantakarta da makotanta da kuma irin rashin jituwa da ke wanzuwa tsakanin wasu 'yan kasar. Ga alama wannan ne ma ya sanya firaministan kasar ta Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kare kansu daga dukannin wata barazana da ka iya kunno musu kai.

Da dama dai na kallon wadannan kalamai na Natenyahu a matsayin gugar zana ko kuma aikewa da sako ga kasashen da ke zaman 'yan marina da kasarsa musamman ma Iran da kuma Falasdinawa da ke cigaba da fafutuka wajen ganin sun karbe 'yanci da wasu yankunan da ke karkashin ikon Isra'ilan wanda suka ce daga hannunsu aka karba da karfin tuwo, batun da ya sanya cigaba da yin zanga-zanga ta ganin sun samu abin da ya ke nasu.

Gazastreifen Autoreifenverbrennung Jugendliche Zuschauer
Matasan Falasdinawa na da fatan sake komawa yankunan kakanninsu na asaliHoto: DW/T. Krämer

To a daura da bikin da Isra'ila din ke yi na murnar zagayowar ranar da ta kai ga girka kasarta, Falasdina kuwa a nasu bangaren wani zama suke yi na alhini da nuna juyayi na rasa matsugunansu da suka yi sakamakon mamaye wani yanki na kasarsu da aka yi. Baya ga wannan Falasdinawa din har wa yau na zama irin na makoki don tunawa da wanda suka rasu sakamakon fafutuka ta kare kasarsu. Wannan ne ma ya sanya wasu 'yan Falasdinun ciki kuwa har da fitacciyar 'yar siyasar nan Hannan Ashrawi cewar dole ne a kullum a cigaba da samun 'yan kasar su tunzura kana su dau matakin da ba shi ke nan ba.