Shekaru 70 da ƙaddamar da hare hare kan Yahudawa a Jamus | Siyasa | DW | 10.11.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 70 da ƙaddamar da hare hare kan Yahudawa a Jamus

Shugabannin Jamus sun yi kira da a daƙile ayyukan masu ƙyamar baƙi da nuna wariya

default

Kantin Yahudawa a Berlin bayan daren 10 ga watan Nuwanban 1938

A dangane da cikar shekaru 70 da fara kai hare hare kan Yahudawa a Jamus abin da ya zama mafarin kisan ƙare dangi da aka yi musu a yaƙin duniya na biyu, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira da a ƙara ɗaukar sahihan matakan yaƙi da masu ƙyamar Yahudawa da baƙi da masu nuna wariyar jinsi.

A ƙarshen zaman juyayi na tsawon makon guda da aka yi a faɗin nan Jamus wanda ya kawo ƙarshe a jiya dac dare, shugabannin wannan ƙasa da ma Yahudawa sun gudanar da addu´o´i a wani wurin ibadar Yahudawa dake Berlin don tunawa da hare haren da aka kai kan Yahudawa daga daren 9 zuwa 10 ga watan Nuwamban shekarar 1938. A jawabin da ta yi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi nuni da cewa a cikin watanni tara na wannan shekara an aikata laifuka masu nasaba da ƙyamar aƙidar Yahudanci kimanin 800 a nan Jamus. ta ce bai kamata a kawar da kai ba idan aka ci zarafin malaman Yahudawa ko kai hare haren akan maƙabartansu ko kuma kwatanta matakan Isra´ila a Zirin Gaza da cewa yaƙin ne na ksian ƙare dangi.

"Bai kamata ƙyamar baƙi, nuna wariyar jinsi da ƙyamar aƙidar Yahudanci su samu gindin zama a Turai ko a ƙasashen Larabawa ko a wasu yankuna na wannan duniya ta mu ba. Bisa la´akari da abubuwan da suka faru a baya, bai kamata mu kama baki mu yi shiru ba."

A nata ɓangaren shugabar majalisar tsakiya ta Yahudawa a Jamus Charlotte Knobloch ta nuna fatan cewa bukin tunawa da wannan ta´asar zai ƙarfafa guiwar Jamusawa wajen nuna juriya da watsi da sabbin aƙidojin masu matsanancin ra´ayin kishin ƙasa.

"A gareni ba zai wadatar ba a yi ta yin kashedi game da masu son raya manufar ´yan Nazi ala misali kamar haramta ayyukan jam´iyar NPD. Ba daidai ba ne idan wani shugaban siyasa ya kwatanta matsalolin hada-hadar kuɗi da ake fama da su yanzu da ta´asar da Nazi suka aikata. Wannan rashin masaniya ta tarihi ba abin karɓuwa ba ne."

Knobloch wadda lokacin da aka aikata wannan ta´asa ta na ´yar shekaru shidda a duniya ta ce ci-gaba da tunawa da wannan aika-aikar alhaki ne da ya rataya kan dukkan masu faɗa a ji a wannan ƙasa.

Ta´asar ta daren tara zuwa 10 ga watan Nuwamban wanda wasu ke yiwa laƙabi da daren fashewar gilashi, ´yan Nazi sun kai hare hare kan kantuna yahudawa da ƙona wuraren ibadarsu kimanin 300 sannan aka tilastawa sama da mutane dubu 30 tserewa zuwa sansanonin gwale gwale.