Shekaru 60 da kai farmakin jiragen saman yakin Amurka da birtaniya a Dresden | Siyasa | DW | 11.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 60 da kai farmakin jiragen saman yakin Amurka da birtaniya a Dresden

A daidai ranar 13 ga watan fabarairun shekarar 1945 ne jiragen saman yakin Amurka da Birtaniya suka shiga yi wa birnin Dresden ruwan bamabamai suna masu halaka mutanen da aka kiyasce yawansu ya kai dubu 35

Birnin Dresden bayan yakin duniya na biyu

Birnin Dresden bayan yakin duniya na biyu

A yammacin 13 ga watan fabararu na shekarar 1945, wacce tayi kacibis da talatar karshe ta bukukuwan Karneval a Jamus, jiragen saman yakin Birtaniya samfurin Lancaster kimanin 244 da kuma samfurin Mosquito guda tara suka taso daga sansaninsu dake kudancin Ingila suka kuma isa samaniyar birnin Dresden a wajejen karfe tara da rabi na dare. Jim kadan bayan haka jiragen suka shiga yi wa birnin ruwan bamabamai, ba ji ba gani kuma a cikin kiftawa da Bisimillah wuta ta kama dukkan sassa na cibiyar birnin na Dresden dake gabacin Jamus. Wannan harin dai yana da nufin karya zuciyar farar fula ne dake nuna juriya duk da wahalar da suke fama da ita da kuma share hanyar kai guzuri ga dakarun sojan kasashen taron dangi, wadanda ke dada kusantar birnin. A wajejen karfe daya zuwa karfe biyu na dare wasu jiragen saman yakin da yawansu ya kai 500 suka sake kai wa wani yankin birnin mai fadin murabba’in kilomita 15 hari. Wata matar da ta gane wa idanuwanta abin da ya faru ta ce an kai farmaki da yawa a gidansu, inda suka yi kwance kuma mijinta ne ya gano cewar gidan fa ya kama wuta. Ala-tilas suka bi cikin wutar domin kubutar da ransu. Hare-haren farko da na biyu da jiragen saman yakin kasashen na Amurka da Birtaniya suka kai sun yi kaca-kaca da cibiyar birnin na Dresden dake da dadadden tarihi. Wadannan hare sun rutsa ne da gidajen mutane da na coci da na gwamnati da kuma na ajiye kayan tarihi, a maimakon sansanonin soja ko masana’antu ko filin saukar jiragen sama dake kurkusa da mayakan sama na Jamus. A kashe gari da tsakar rana jiragen saman yakin Amurka suka sake gabatar da matakinsu na a sha-ruwan tsuntsaye, inda suka yi tsawon mintuna goma suna wa muhimman hanyoyin zirga-zigar motoci da jiragen kasa ruwan bamabamai. Kawo yanzun dai babu wasu takamaimun alkaluma da aka bayar a game da yawan mutanen da suka halaka sakamakon wadannan hare-hare, domin kuwa a daidai wannan lokaci birnin Dresden na karbar bakuncin dubban daruruwan ‚yan gudun hijira. Wannan mataki ya zama wata shaida game da ta’asar hare-haren jiragen saman yaki. Al’umar Dresden ba su yi wata-wata ba wajen tashi gadan-gadan domin sake gina birnin nasu da jiragen saman yakin Amurka da na Birtaniya suka yi kaca-kaca da shi bayan kawo karshen yakin. Babbar shaidar haka ita ce mujami’ar da ake kira Frauenkirche, wacce aka yi tsawon shekaru 50 ba a dauki wani matakin sake gina ta ba domin ta zama gargadi da kuma alamar barna da kashe-kashe. Bayan hadewar gabaci da yammacin Jamus an sake gina mujami’ar a bisa suffarta ta asali.