1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shekaru 60 da kafa hukumar UNESCO

Hukumar UNESCO ta majalisar dinkin duniya tayi shekaru sittin tana kyautata al'adu a duniya baki daya

UNESCO ta cika shekaru sittin

UNESCO ta cika shekaru sittin

Shekaru sittin da suka wuce, wato a ranar sha shidda ga watan Nuwamba na shekara ta 1945, aka kafa hukumar UNESCO, hukumar kula da ilimi kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya. A daidai wannan lokaci, duniya gaba daya ta kasance cikin mummunan hali ne, jim kadan bayan kare yakin duniya na biyu. A wnanan lokaci, mutane sun maida hankalin su ga neman yadda zasu rayu, amma ba yadda zasu raya al’adu, karkashin inuwar majalisar dinkin duniya ba. To amma wadanda suka kafa hukumar ta UNESCO sun yi tambayar, shin duk da halin da aka kasance a ciki a wancan lokaci, zai yiwu al’ummar duniya su ci gaba da yin watsi da al’adun su? Umaru Aliyu ya fasara rahoton wakiliyar DW Helle Jeppesen, game da rayuwar shekaru sittin da hukumar ta UNESCO.

To wadanda suka kafa wannan hukuma sun kai ga fahimtar cewar tun da shike yake-yake a zukatan masu neman tayar dasu ake fama tunanin su, saboda haka zaman lafiya ma, a zukatan mutane za’a iya tabbatar da shi. Wannan tunani ma, yana daya daga cikin tsare-tsaren dake kunshe a kundin da ya kafa hukumar ta Unesco ranar goma sha shidda ga watan Nuwamna na shekara ta 1945. Har yanzu kuwa, ana ci gaba da samun yake-yake tsakanin kasashe da dama a ko ina cikin duniya, kuma kamar yadda shugaban kasa na Jamus, Horst Köhler ya nunar a jawabin sa a zauren babban taron hukumar ta Unesco, lokacin bikincikar ta shekaru sittin a Paris: mutuncin dan Adam dai har yanzu yana fuskantar mummunan hadari a fannoni da dama: ga yunwa ga rashin ci gaba da rashin yanci ga kuma fama da ake yi da aiyukan tarzoma. To amma duk da haka, kamar yadda shugaban na Jamus yace: dan Adam bai kyale wadannan abubuwa sun sha masa kai ba. Yace:

Muna da kungiyoyi na duniya baki daya, kamar UNESCO, wadanda manyan aiyukan da suka sanya a gaba, suka hada har da kare daraja da mutuncin dan Adam da kyautata hadin kai da zaman tare ta fuskar al’adu. Muna da kungiyoyin duniya da suke da sha’awa tare da nuna damuwa ga abin dakan shafi yan Adam da makomar al’adu dake cikin mummunan hali sakamakon amfani da karfi da aiyukan rashin gaskiya da talauci da rashin hakuri da juna.

Tun bayan da aka kafa kungiyar ta Unesco, babban aikin ta dai shine kare al’adu masu yawa da suka banbanta da juna a ko ina cikin duniya. Duk wanda aka tambaye shi ma’anar UNESCO, abin yakan ce shine, hukuma ce ta majalisar dinkin duniya, ko kuma hukuma ce mai kula da al’adu, tare da mantawa da gaskiyar cewar bayan al’adun, hukumar takan kuma kula da fannoni na ilimi, da kimiyya. Hukumar Unesco dai ita ce tushen kaddamar da kampe din nan na tabbatar da ilimi ga kowa da kowa. Tun a shekara ta 1948, hukumar tayi kira ga kasashe wakilan ta, su tabbatar da baiwa ko wane yaro ko yarinya ilimi akalla zuwa karshen matakin farko. A yanzu haka, hukumar tana tafiyar da kampe karkashin taken, ilimi ga kowa da kowa, wanda shiri ne tun daga shekara ta 2003, zuwa tsawon shekaru goma, bisa manufar bunkasa ilimi a duniya baki daya. Kasashen hukumar ta Unesco, a lokacin taron su a Dakar a shekara ta 2000, sun daidaita a kann wani tsari mai fannoni takwas, wanda suka ce shine burin su na ilmantar da al’ummar duniya, nan da shekara ta 2015. Daga cikin wadanan fannoni kuwa, har da bayar da ilimi mai nagarta, kuma kyauta ga ko wane matashi, namiji ko mace da rage yawan marasa ilimi da misalin kashi hamsin cikin dari da daidaita matsayin tsakanin maza da mata a fannin ilimi.

Wani rahoto da aka gabatar a London a a makon jiya, ya nuna cewar samun ilimi akalla na piramare, batu ne dake bukatar namijin kokari, bama a tsakanin yara kadai ba, amma har idan ana son tabbatar da ilimin yaki da jahilci tsakanin magidanta. Mutane fiye da miliyan dari bakwai da saba’in ne a duniya baki daya, basu iya mkaratu da rubutu ba.

Darektan hukumar Unesco da ya rubuta wnanan rahoto, Nicholas Burnett yace duka da haka, an sami ci gaba a fannin na baiwa magidanta ilimin yaki da jahilci, alal misali a kasar China, wadda a yan shekarun baya-bayan, nan ta sami nasarar rage yawan al’ummar ta da basu iya karatu da rubutu ba, da misalin miliyan dari.

A bangaren al’adu, daga cikin muhimman gine-gine da hukumar Unesco ta tabbatar dasu a matsayin muhimmai a kasashen da suke, har da ginin mnan na Taj Mahal a India ko kuma ginin mujami’ar birnin Cologne wato Dom. Kazalika, hukumar ta ware wurare fiye da dari bakwai a matsayin wurare na al’adu, masu muhimmanci ga rayuwar dan Adam.