Shekaru 60 da kafa babbar mashawartar MDD | Siyasa | DW | 10.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 60 da kafa babbar mashawartar MDD

A ranar 10 ga watan janairun 1946 ne babbar mashawartar MDD yayi taronsa na farko

Shelkwatar MDD

Shelkwatar MDD

Kwanaki 147 kacal bayan kawo karshen yakin duniya na biyu babbar mashawartar MDD ta kammala taronta na farko da ya samu halarcin kasashe 51, wadanda suka yi fatan samar da wani sabon yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniyar karkashin tutar wannan majalisa. Paul Henrik Spaak, ministan harkokin wajen kasar Belgium a wancan lokaci shi ne ya shugabanci zaman taron. To sai dai kuma tun tafiya ba ta je nesa ba aka fara fuskantar wata tangarda, wacce ta so ta jefa majalisar dinkin duniyar cikin wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi game da makomarta. Domin kuwa ko da yake a zahiri al’amuran na tafiya salin-alin, amma a bayan fage ta kasance tana kasa tana dabo. Jim kadan kafin a zabi tsofon ministan harkokin wajen kasar Belgium wakilin daular tarayyar Soviet a MDD Andrei Gromyko ya nemi tsayar da wani dan takarar da zai kalubalance shi. Shi kansa sakatare-janar na farko da aka nada Trygve Lie daga kasar Norway sai da yayi batu a game da wani mummunan yanayi na gardandami da sabani da aka gabatar da taron babbar mashawartar ta MDD karkashinsa. Shi kuwa kwamitin sulhu yayi zamansa na farko ne bayan da aka zabi wakilai da ba na dindindin ba tare da tsayar da shawarar tabbatar da shelkwatar majalisar a birnin New York.

A ranar 24 ga watan janairu na 1948 ne babbar mashawartar ta MDD ta gabatar da kudurinta na farko, wanda ke yin kira game da lalata miyagun makamai na kare dangi. Ba a kuwa dade ba aka fara fuskantar gurbacewar yanayin dangantaku tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet, inda kasashen biyu suka mayar da babbar mashawartar MDDr tamkar wani dandali na parpagandarsu ta yakin cacar baka. A karkashin wannan mummunan yanayi na yakin cacar baka ne aka karbi kasashen Jamus ta Gabas da ta Yamma a inuwar MDD a shekara ta 1973. Ga dai abin da ministan harkokin wajen JTG na wancan lokaci, Otto Winzer yake cewa:

„Karbar Janhuriyar Demokradiyyar Jamus a MDD wani muhimmin lamari ne na tarihi da al’umar kasar ba zasu taba mantawa da shi tsawon rayuwarsu ba.

Shi ma tsofon shugaban gwamnatin Jamus ta Yamma Willy Brandt yayi bayani yana mai cewar:

„Kaifin hankalin da Allah Yayi wa dan-Adam shi ne ya taimaka aka kirkiro wannan majalisa ta dinkin duniya. Kazalika wannan basirar ce ta sanya dan-Adam ya fahimci cewar wannan majalisa abu ne da ba makawa game da shi.“

Kuma ko da yake wasu daga cikin shuagabannin Amurka ‚yan jam’iyyar Republicans kann kwatanta babbar mashawartar tamkar wani dandali na fadi-ka-huta, kuma galibi ba a wajabta aikin kudurorinta akan kasashe, amma fa mashawartar ‚yar shekaru 60 ta dade tana mai taka muhimmiyar rawa a siyasar duniya.