Shekaru 60 bayan jefa atam bam a kan birnin Hiroshima, ina aka nufa ? | Siyasa | DW | 05.08.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 60 bayan jefa atam bam a kan birnin Hiroshima, ina aka nufa ?

Tun lokacin mulkin shugaba John F. Kennedy na Amirka ne, ake ta tattauna batun hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, saboda mummunan sakamakon da jefa atam bam da aka yi a kan biranen Hiroshima da Nagasaki a kasar Japan ta haifar. Duk da munin abin da ya auku, har ila yau dai gamayyar kasa da kasa ba ta cim ma shawo kan duk kasashe masu mallakar makaman nukiliyan da masu neman mallakarsa su yi watsi da wannan burin ba.

Birnin Hiroshima, a ragargaje, bayan jefa mata atam bam, da jirgin saman yakin Amirka kirar B-29 ya yi, a ran 6 ga watan Agusta ta shekarar 1945.

Birnin Hiroshima, a ragargaje, bayan jefa mata atam bam, da jirgin saman yakin Amirka kirar B-29 ya yi, a ran 6 ga watan Agusta ta shekarar 1945.

Batun yaduwa da mallakar makaman nukiliya a duniya dai, tun karshen yakìn duniya na biyu ne aka fara yin muhawara a kansa don kago hanyoyin kawad da su ma gaba daya daga doron kasa. Bayan an kafa Majalisar Dinkin Duniya, dab da karshen yakin ne, kasashe 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar, suka fara shawarwari game da yadda za su haramta da kuma hana yaduwar wadannan makaman zuwa sauran yankuna na duniya. Sai dai su da kansu ba su haramta wa kansu mallakar makaman ba.

A cikin shekarar 1968 ne, rukunin na kasashe 5 masu mallakar makaman nukiliya, wato Amirka, da Sin, da Rasha, da Faransa da Birtaniya suka cim ma wata yarjejeniya tsakaninsu, inda suka dau alkawarin hana sayar wa duk wata fasaha da kuma kayayyakin da za a iya yin amfani da su wajen sarrafa makaman na nukiliya.

A shekarar 1970 ne kuma, kasashe kusan dari da 90 na Majalisar Dinkin Duniyar, suka amince da yarjejeniyar, wadda aka fadada ta suka kuma sanya hannu a kanta.

Don sa ido kan ganin cewa, an kiyaye ka’idojin wannan yarjejeniyar ne, aka kafa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar dinkin Duniya, wadda ke da cibiyarta a birnin Vienna na kasar Austriya. Ita dai wannan hukumar, ita ce ke gudanad da bincike a duk kasashen da ke da tashoshin makamashin nukiliya. A karshen shekara ta 2003 dai, yawan wadannan kasashen ya kai 44. Don dai tabbatar da cewa, an inganta hanyoyin gudanad da binciken da ake yi ne, aka fadada ka’idojin yarjejeniyar a shekarar 1997, don ta kunshi wasu kudurorin da ke bai wa hukmar damar tura jami’anta zuwa kasashe don su gudanad da binciken ba tare da ba da sanarwa ba tun da farko. Kawo yanzu dai, kasashe 80 na Majalisar Dinkin Duniya ne suka hanya hannu kan karin da aka yi wa yarjejeniyar. Kasar Iran, wadda a halin yanzu ake ta jayayya da ita kan manufofin da ta sanya a gaba, na mallakar makamashin nukiliya, na cikin wadanda suka sanya hannu a kan wannan yarjejeniyar.

A zayyane dai, yarjejeniyar na da ma’ana, saboda za ta iya hana yaduwar makaman nukiliyan. Amma a zahiri, akwai giyabu da yawa da kudurorin yarjejeniyar ba su iya sun cike su ba, har ila yau. A lal misali, akwai tabbatattun kasashe masu mallakar makkaman nukiliyan; akwai kuma wadanda ba su bayyana hakan ba a hukumance ko kuma bisa manufa. Har ila yau dai, akwai kuma kasashen da ake zaton suna da makaman nukiliyan, ko kuma wadanda ke yunkurin mallakarsu, ko kuma wadanda ake tuhuma da kokarin yin hakan. To gudanad da bincike a kan duk wadannan nau’o’i na kasashen da ke da wata jibinta da mallakar makaman nukiliyan, shi ne abin da ke ci wa hukumar Kula da makamashin nukiliyan ta Majalisar Dinkin Duniya tuwo a kwarya.

Da can dai, kasar Iraqi karkashin mulkin Saddam Hussein, na cikin kasashen da ake tuhumarsu da yunkurin mallakar makaman na nukiliya, tare da taimakon Faransa, wadda ke cikin kasashe 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar. Kafin tashar makamashin nukiliyan da Iraqi ta ginan ya fara aiki a cikin shekarar 1981 ne, Isra’ila ta kai mata harin bamabamai da jiragen samanta, ta kuma ragargaza ta.

Daga bisani ne dai kuma, Amirka ta yi amfani da wannan zargin don hujjanta afka wa Iraqin da ta yi, duk da cewa har ya zuwa yanzu, babu tabbatacciyar hujjar da ta kawo ta nuna cewa, lalle Iraqin ta mallaki makaman nukiliya.

Isra’ilan da kanta ma, tana da tashar makamashin nukiliya, wadda ita ma tare da taimakon Faransan ne ta gina ta a Dimona. Har ila yau dai, Isra’ilan ba ta fito fili ta bayyana cewa tana da makaman nukiliyan ba. Amma shakka babu, duk da daure mata gindi da Amirka ke yi.

Kasashe kamarsu Indiya da Pakistan ma sun shiga sahun masu mallakar makaman nukiliyan.

 • Kwanan wata 05.08.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvac
 • Kwanan wata 05.08.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvac