1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 6 da harin ta´addanci a Amirka

September 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuBn

A yau talata shekaru 6 daidai bayan hare haren ta´adancin ranar 11 ga watan satumban shekara ta 2001, Amirka zata yi bukin tunawa da mutane kimanin dubu 3 da suka rasa rayukansu a wadannan hare hare. A karon farko a birnin New York ba za´a yi wannan buki a daidai wurin da a da tagwayen gine ginen na cibiyar kasuwanci ta duniya suke ba. A dangane da aikin ginin da ake yi a wurin da aka fi sani da Ground Zero, za´a gudanar da bukin a wani wuri dake kusa. Za´a yi shiru na minti daya da misalin karfe 8 da minti 46 agogon New York wato a daidai lokacin da jirgin saman farko ya afkawa ginin. Shugaban Amirka GWB zai halarci wurin bukin addu´o´i da za´a yi a birnin Washington.