1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 da samun 'yanci kai a Lesotho

October 4, 2016

Kasar Lesotho ta cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga Birtaniya sai dai har yanzu ana ganin akwai aiki a gaba musamman batun sakarwa 'yar kasar mara domin samun cikakken 'yanci na gudanar da mulki a kasar baki daya.

https://p.dw.com/p/2QrPd
Lesotho Premierminister Pakalitha Bethuel Mosisili bei der Generalversammlung der UN
Hoto: picture alliance / AP Photo

A ranar hudu ga watan Afrilun shekara ta 1966 ne dai Lesotho ta samu 'yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka na Birtaniya sai dai a yayin da kasar ke bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai masu fafautuka na kokawa dangane da yada suka ce har yanzu a bangaren siyasa kasar ba ta je ko ina ba. Wani dan kungiyar farar hula mai suna Lenka Thamae ya ce "muna samun matsaloli masu yawa da suka danganci ta ke hakkin dan Adam da sojoji ke yi wanda kuma suke samun goyon bayan mahukunta. Gaskiya zamu iya cewa a yanzu dimokaradiyyarmu na hannun sojoji"

Lesotho Feier während einer Eröffnungszeremonie in Maseru
Al'ummar Lesotho na murnar cika shekaru 50 da samun 'yancin kai duk kuwa da cewar kasar na fuskantar tarin matsaloli ciki kuwa har da na tattalin arzikinHoto: AFP/Getty Images

Wani abu har wa yau da bai samu cigaba na a zo a gani ba shi ne tattalin arzikin kasar domin kuwa kaso 95 cikin 100 na kayan masarufi da al'ummar Lesotho ke amfani da su ana shigo da su ne daga makwabciyar kasar wato Afirka ta Kudu, kana kudin shigarta ya dogara ne daga wata yarjejeniyar sayen tufafi da suka kulla da Amirka sannan kasar ta dogara ne kacokan kan tallafin raya kasa da ta ke samu daga kasashen ketare.

To yayin da wannan kasa ke samun tallafi daga wasu kasashen, ita ma a nata bangaren ana amfana da ita. Alal misali Afirka ta Kudun na cin gajiyar ruwan da kasar ke da shi kasancewar kaso 40 cikin 100 na ruwan da rukunin masana'antun Afirka ta Kudun ke samu na fitowa ne daga dam din Lesotho to sai dai wannan tsari na kama da abin nan da ake cewa kura da shan bugu gardi da amshe kudi domin kuwa Afirka ta Kudun ba ta baiwa Lesotho din wata dama da cimma yarjejeniya bisa adalci kamar yadda 'yan fafutuka ke bayyanawa.