Shekaru 40 Sarki Qaboos yana mulki a Oman | Siyasa | DW | 23.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 40 Sarki Qaboos yana mulki a Oman

Sarki Qaboos ya sabunta ƙasarsa a zamanin mulkinsa

default

Sultan Qaboos bin Said na Oman

Shekaru 40 kenan cur da Sarki Qaboos na ƙasar Oman ya ɗare kan karagar mulki bayan da ya tuntsurar da mahaifinsa Sultan Sa'id Ibn Taimur ya kuma tilasta masa yin gudun hijira, domin kawo sauyi a ƙasar, wanda a lokacin mulkin mahaifin nasa ta yi zaman saniyar ware a duniya, sakamakon mulkin danniya da matsalar rashin ci-gaban rayuwa da kuma fataucin bayi . Sarki Qaboos ya ɗare kan karagar mulkin ne a ranar 23 ga watan Yulin shekarar 1970 a lokacin da ya koma gida bayan samun horo na aikin soja a ƙasahen Birtaniya da kuma nan Jamus.

A shekarar 1970 ne Qaboos ya tilasta wa mahaifinsa yin ritaya a lokacin da ya koma gida, bayan gama samun horo na aikin soja a birnin Sandhurst na ƙasar Birtaniya, ya kuma yi aiki da sojin Birtaniya a nan Jamus. Mahaifin nasa dai ya rasu ne shekaru biyu bayan yin gudun hijra a ƙasar Birtaniya. A wannan lokaci kuma, ƙasar Oman ta fara farfaɗowa daga koma baya daidai da yadda sarki Qaboos ya buƙata.

"Zan yi bakin ƙoƙarina domin samar da jin daɗin rayuwar al'ummar wannan ƙasa, tare da kyautata makomarsu, inji Sarki Qaboos. Wannan kuwa wata manufa ce da ba zamu iya cimma ba face da taimakon ɗaiɗaikun 'yan ƙasa".

Sabon Sarkin na Oman dai ya tashi haiƙan domin kau da mulkin kwaminisanci da aka yi fama da shi a wancan lokaci a wannan ƙasa da ke kudancin ƙasar Yaman tare da neman ci gaban wannan yanki ga baki ɗaya. Daga nan aka fara gina hanyoyin sufuri da makarantu da asibitoci tare da yin kira ga ƙwararrun ƙasar da suka haɗa da waɗanda ke tsibirin zanzibar da su koma gida. Sai da kuma aka gayyaci mashawarta daga ƙasa da ƙasa da suka haɗa da Jamus, waɗanda sarkin yayi aiki da su kafaɗa da kafaɗa.

Sultanat Oman Tourismus

Cikin fadar sarki

Ko shaka babu, ƙasar Oman ta buɗe ƙofofinta a ƙarƙashin mulkin Qaboos ta inganta wuraren yawon buɗe ido da al'adunta na gargajiya da kuma kare albarkatun hallitta. Ga baki ɗaya, an gudanar da ayyuka da dama domin samar da ci gaban sassa daban daban, musamman na aikin man fetur da kuma gas.

Bugu da ƙari an kuma samar da daidaituwa tsakanin mata da maza kamar yadda tsohuwar mambar majalisar Shura ta wannan ƙasar, Shuroor Mohammed Al- Ghammary ke cewa:

"An daidata tsakanin mata da maza. Babu wata doka da ke kawo cikas ga mata wajen yin duk abin da suke so walau a ma'aikatun gwamnati ko kuma wajen neman ilimi da ma ko ina".

Oman Autostraße zwischen Muskat und Nizwa

Hanya ta zamani tsakanin biranen Muskat da Nizwa

A ƙarƙashin Qabbos ƙasar Oman ta inganta dangantakarta da sauran ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita, da suka haɗa da Saudi Arabiya da Iran da ma ƙasashen yamma irinsu Amirka da Birtaniya. A baya ga haka, Sarki Qaboos na matuƙar nuna adawa da matsanancin ra'ayi na kowane iri:

Yace "A nan ƙasar muna ɗaukar matakai na dakile tsauraran ra'ayoyi na kowane iri da suka hada da na addini".

Sarkin na Oman ya bayyanar da sha'awarsa ga aladu: A don haka ne ma ya kafa wata kƙngiyar kiɗe -kiɗe da bushe-bushe na gargajiya. Sai dai kuma duk da haka akwai ayar tambaya game da rashin dimukuraɗiya a wannan ƙasa . A dangane da haka wani ɗan Birtaniya da ke bai wa gwamnatin Oman shawara ya ce abin da ƙasar ke buƙata shi ne sarauta ta ƙwarai amma ba dimukuraɗiya ba.

Mawallafi: Halima Abbas

Edita: Umaru Aliyu