Shekaru 30 da hadarin nukiliya | Labarai | DW | 26.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru 30 da hadarin nukiliya

A Ukraine ana cika shekaru 30 da hadarin nukiliya na Chernobyl mafi muni da nuniya ta fuskanta tun bayan yakin duniya lokacin kasar tana karkashin tsohuwar Tarayyar Soviet.

A wannan Talata a Ukraine ana cika shekaru 30 da hadarin nukiliya mafi muni da duniya ta fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu da ya faru a Chernobyl abin da ya kai ga mutuwar dubban mutane, sannan ya janyo sake tunani kan yadda ake tafiyar da harkokin da suka shafi nukiliya.

Fiye da ton 200 na uranium ya fice daga cikin lalataccen abin da ake sarrafa nikiliya ya shafi sassan Turai, inda cikin kwanaki 10 ya haifar da wani mummunan sakamako.