Shekara tara bayan haren-haren 11 ga satumba
September 11, 2010A ƙasar Amirka, a daidai lokacin da ake juyayin cika shekara tara da haren-haren nan na 11 ga watan satumba da ya kashe mutane dubu uku, mahawara na ci gaba da zafafa dangane da gina masallaci a kusa da inda aka kai harin. Gangamin nuna goyon baya da kuma na nuna adawa sun fara gudana a kusan da tagwayen gine-ginen na birnin New-York da haren-haren suka ritsa da su.
Wannan dai shi ne karon farko da aka samu ruɗani irin daban daban tun bayan ƙaddamar da jerin hare-haren da ƙungiyar Al-qa'ida ta yi a wasu mahimman gine-gine na ƙasar Amirka. Barazanar ƙona alƙur'ani mai tsarki da pastor Terry Jones ya yi na daga al'amura da ke haifar da saɓani.
Shugaba Barack Obama na shirin isa ma'aikatar tsaron Amirka wato Pentagon domin halartan bikin nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren na sahekaru taran da suka gabata. An gudanar da addu'o'i a kusa da inda hare-haren suka wakana a birnin New-York.
Mawallafi:Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala