Shekara guda da kisan Hariri | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekara guda da kisan Hariri

A yau kasar Lebanon take bikin zagayowar shekara guda da kashe tsohon Firaminista Rafik Hariri.

Zaa dai gudanar da babban gangami a babban birnin kasar Beirut.

An dai kashe Hariri ne cikin wani harin bam a ranar 14 ga watan fabrairu na shekarar data gabata.

Kisan nasa kuwa ya janyo zanga zanga akan titunan kasar,wadda gami da matsin lamba daga kasashen ketare,suka sanya kasar Syria ta janye sojojinta daga Lebanon,bayan shekaru 30 da kasancewarsu a can.

Wani bincike da MDD ta gudanar game da kisan Hariri,ya ce da hannun Syria da kuma wasu jamian gwamnatin Lebanon cikin kisan Hariri.