Shekara guda bayan kazamar zanga zangar Faransa | Siyasa | DW | 27.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara guda bayan kazamar zanga zangar Faransa

Daruruwan matasa a yankunan unguwannin baki a Faransa sun gudanar da bikin alhini ta zagoyowar shekara da aukuwar hargitsin shekarar 2005 a Faransa.

Zanga Zangar lumana ta Matasa a Faransa

Zanga Zangar lumana ta Matasa a Faransa

Ɗaruruwan matasa sanye da riguna wanda aka yiwa rubutu da laƙabin “Mutuwa ba tare da haƙƙi” ba, sun yi fara yin dandazo ne a yankin unguwannin baƙi na Clichy-sous-Bois, dake kusa da birnin Paris domin zanga zangar lumana ta zagayowar cikar shekara guda da wasu matasa biyu suka rasa rayukan su sakamakon ƙonewa da ƙarfin wutar lantarki

Magajin garin Clichy-sous-Bois Claude Dilain tare da iyalan matasan biyu da suka riga mu gidan gaskiya suka jagoranci tawagar ɗaruruwan matasa inda suka yi tattaki ya zuwa tashar Transfomar da matasan biyu suka gamu da ajalin su.

Su dai matasan sun gamu da ajalin nasu ne bayan da `yan sanda suka biyo su da gudu wanda ya kai su ga faɗawa tashar wutar lantarkin domin kuɓuta daga yan sandan. Ba tare da wata-wata ba, ƙarfin wutar lantarkin ta ja su inda kuma nan take suka ce ga garin ku nan. Wannan lamari ya haifar da mummunan zanga zanga a kusan dukkan manyan birane a faɗin ƙasar Faransa wanda ya tilastawa gwamnatin P/M Dominique de Villepin sanya dokar ta baci a waɗannan unguwanni.

An yi kiyasin hasarar dukiya mai yawa ta kwatankwacin euro miliyan 160, kimanin dala miliyan 200, bugu da ƙari motoci kimanin 10,000 ne da gidaje kusan 300 masu zanga zangar suka ƙone ƙurumus.

A jawabin sa bayan wannan tarzoma, shugaban ƙasar Faransa Jaques Chirac ya yi Allah wadai da aƙidar nuna wariya tare da yin kashedin cewa gwamnati ba zata lamunta da karya doka da oda ba.

A hannu guda dai taron gangamin na yau, ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman zulumi a wasu unguwannin baƙi a ƙasar Faransan bayan aukuwar tarzoma a yan makwannin nan wanda ya haɗa da arangama tsakanin gungun matasa da yan sanda tare da ƙona motoci masu yawa.

Rafika Benguedda wani dalibi mai shekaru 21 da haihuwa, yace shekara guda bayan wannan hargitsi, har yanzu babu abin da ya sauya, inda suka koka da cewa ana nuna musu wariya ga kuma ɗan karen talauci da yankunan baƙin ke fama da shi.

A halin da ake ciki Ministan kula da alámuran cikin gida na ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy, ya bada umarnin tsaurara matakan tsaro a motocin Bus Bus a yankunan unguwannin baƙi a faɗin ƙasar domin kare aukuwar tashin hankali.

A waje guda kuma P/M Dominique de Villepin ya kare gwamnatin sa a game da zargin da ake mata na rashin samar da abubuwan buƙatun rayuwa a yankunan unguwannin baƙi. Yace ina ji nan da can ana cewa gwamnati ba ta yi komai ba wajen inganta rayuwar jamaá a yankunan baƙi dake kewaye da biranen Faransa, wannan ba gaskiya bane, a zahirin gaskiya gwamnati na bakin ƙoƙarin ta, matsaloli mun san akwai su, amma ba yanzu suka faro ba, kuma ba zaá iya magance su a lokaci guda ba sai a hankali.