1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda bayan faruwar Tsunami

December 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvEu

Da yawa daga cikin al´ummomi na duniya naci gaba da nuna alhini ga iyalan wadanda igiyar ruwa ta tsunami tayiwa lahani a yankin Asia da kuma wasu kasashe na Afrika.

Shekara guda bayan fuskantar wannan mummun balá´i an kiyasta cewa mutane dubu dari 223 ne suka rasa rayukan su banda wasu sama da haka da suka jikkata.

Rahotanni da suka iso mana sun nunar da cewa da yawa daga cikin kasashen da wannan abu ya shafa sun gudanar da addu´oi tare da shiru na dan mintuna kadan don tunawa da wadanda suka rasa rayukan su bayan faruwar wannan bala´i.

A yayin da ake ci gaba da bukukuwan nuna alhinin, a waje daya kuma ministar bayar da tallafin raya kasashe ta Jamus, wato Heidemarie Wieczoreck Zeul cewa tayi, Jamus ba zata taba mancewa da mutanen da suka rasa rayukan su a sakamakon wannan bala´i na tsunami ba, a don haka kasar zata ci gaba da kokarin ganin ta samar da wata na´ura ga wannan yanki na Asia da zata dinga bada bayanai game da bala´oi dake da nasaba da igiyar ruwan ta tsunami don daukar matakin daya dace cikin gaggawa.l