1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara daya da nada Hosrt Köhler a matsayin shugaban kasar Jamus

YAHAYA AHMEDJuly 1, 2005

A ran 1. ga watan Yuli ne shugaban kasar tarayyar Jamus Horst Köhler ya cika shekara daya da nada shi a wannan mukamin da aka yi. A cikin tarihin Jamus tun yakin duniya na biyu kuma, shi ne shugaban kasa na 9, kuma shi ne farkon shugaban da ya taba hawar wannan mukamin ba tare da rike wasu mukaman siyasa kafin hakan ba.

https://p.dw.com/p/Bvaz
Shugaban kasa na tarayyar Jamus, Horst Köhler.
Shugaban kasa na tarayyar Jamus, Horst Köhler.Hoto: AP

A lokacin da aka nada shi tamkar sabon shugaban tarayyar Jamus, yau shekara daya daidai ke nan da ta wuce, Horst Köhler ya bayyana cewa, ba zai yi shugabancin son zuci ba. Idan ya ga wasu kurakuran da `yan siyasa ke yi, zai fada musu gaskiya, komin dacinta kuma. Bai kuwa yi wata wata ba, wajen cika wannan alkawarin.

A tsawon shekara dayan nan dai, ya takalo batutuwa da dama da ba su da dadin ji ga Jamusawa, kamar abin da ya kira ragwancin da suke nunawa wajen huskantar kalubalen da kafofin siyasa da na tattalin arzikin kasarsu ke fama da shi. Musamman ma dai, ya yi suka ga halin da wasu Jamusawa ke nunawa na yin amfani da kudaden hukuma wajen biyan bukatunsu, duk da cewa ba sa bukatar wani taimako daga hukuma.

A nan dai ya yi wa Jamusawa da yawa susa inda yake yi musu kaikayi. Sabili da haka ne kuma akka yi ta samun sukar lamirinsa daga bangarori da dama na al’umman wannan kasar. A lal misali kungiyoyin kwadago sun yi ta zarginsa da yunkurin kare maslahar `yan jari hujja, duk da cewa shi da kansa ya sha sukar halayen da wasu manajojin kamfanoni ke nunawa na rashin nuna zumunci ga ma’aikatansu.

Shi dai Horst Köhler, ta daurin gindin jam’iyyun adawa na CDU da FDP ne ya sami hawar wannan mukamin. Sabili da haka ne kuwa `yan jam’iyyun SPD ta gwamnatin tarayya, da damansu ke juya masa baya. A ko yaushe kuma, idan suka sami wata dama, ba sa duban bakin gatari wajen yi masa suka.

Amma duk da hakan dai, kwarjininsa bai dusashe ba a bainar jama’a. Duk da cewa, ba shugaba ba ne mai cikakken iko, yana iyakacin kokarinsa wajen ba da tasa gudummuwa ga tsara manufofin siyasa a nan kasar. Ya dai fito fili ya nuna goyon bayansa ga shirye-shiryen yi wa tsarin tattalin arziki da na wasu karfofin siayasa sauyi, da shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder ya gabatar. Yana kuma cikin masu tofa albarkacin bakinsu ga muhawarar da ake yi a kan fadada shirin canje-canjen don ya shafi duk kafofin siyasar Jamus baki daya.

Matsayin da zai dauka, idan majalisa ta ka da kuri’ar kin amincewa da gwamnatin shugaba Schröder, shi ne zai tabbatad da gudanad da sabon zabe, shekara daya kafin cikar wa’adin gwamnatin tarayyar ta yanzu, ko kuma rashin yin hakan. Idan dai shugaban ya yanke shawarar kin rusa majalisa, don share fagen gudanad da sabon zabe, to zai saba wa manufar janyo sauyi ga kafofin Jamus da shi da kansa ke goyon bayanta. Amma a bangare daya kuma, zai iya yin amfani da wannan ikon nasa, wajen nuna wa duk `yan siyasar kasar nan cewa, a kan wasu batutuwan fa, babu makawa sai an dama da shi.

Kafin a zabe shi, Horst Köhler, ya taba bayyana cewa, yana ganin hawarsa a mukamin shugaban kasa zai kasance wani muhimmin gishiki ne a tarihin Jamus na wannan zamanin.

Bisa dukkan alamu dai, watakila yana da gaskiya a kan wannan batun.