Shekara daya da aukuwar ambaliyar igiyar ruwan Tsunami
December 25, 2005Talla
An fara gudanar da bukukuwan zagayowar shekara guda da aukuwar mummunar ambaliyar igiyar ruwan ta Tsunami a Thailand da kuma wasu kasashen yankin Asiya. A jiya asabar wadanda suka tsira daga wannan bala´i da kuma ´yan´uwan wadanda suka rasu sun ajiye furanni tare da yin addu´o´i a tsibirin Phuket dake kasar Thailand. Kimanin mutane dubu 230 aka kiyasce sun rasu sakamakon bala´in na ambaliyar igiyar ruwan da ta auku kasashen dake gabar tekun Indiya a ranar 26 ga watan desamban shekara ta 2004.