Shekara ɗaya da ´yancin kan Kosovo | Siyasa | DW | 17.02.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara ɗaya da ´yancin kan Kosovo

Yau shekara guda kenan da yankin Kosovo ya samu ´yancinsa wanda hakan ya sa ta zama jaririyar ƙasa a Turai.

default

Bukin cika shekara ɗaya da ´yancin kan Kosovo

To sai dai murnar da aka yi da farko ta koma ciki domin har yanzu babu wani canji ko na misƙala zarratin da aka samu a ƙasar musamman a fannin tattalin arziki inda al´umar ƙasar ke fuskantar matsaloli iri daban daban.

Lokacin wani faretin soji kenan a sansanin rundunar Bundeswehr ta Jamus daek aiki ƙarƙashin lemar dakarun ƙasa da ƙasa na KFOR a Prizren na Kosovo, inda rundunar sojin ta Jamus ta miƙawa dakarun tsaron Kosovo kyautar motocin soji guda 200. Wannan wata gagarumar kyauta ce daga Jamus ga dakarun tsaron ta Kosovo mai ƙabilu daban daban. Shekara guda bayan samun ´yancin kanta, har yanzu wannan jaririyar ƙasar a Turai ba ta samu abin da za a kira da cikakken ´yancin kai ba duk da ɗokin da ɗaukacin Albaniyawan Kosovo ke yi na shiga wannan sabon babi a tarihin ƙasarsu.

A wannan rana ta zagayowar ranar ´yancin da yawa na saka ayar tambaya game da fa´idar wannan ´yanci, kamar yadda wannan matashin a birnin Pristina ya nunar.

"Shekara guda bayan samun ´yancin ya kamata mu yi alfahari da kai wannan matsayi na samun ´yanci da kuma amincewa da mu da manyan ƙasashen duniya suka yi. In baya ga wannan ban ga wata fa´ida da muka samu ba."

Wani direban tasi wanda ke a cikin cunƙoson jerin motoci tofa albarkacin bakinsa yayi yana cewa.

"Gaskiya na sanya dogon buri musamman a fannin samar da abubuwan jin daɗin jama´a da kuma na tattalin arziki. Har yanzu matsalar talauci na ci-gaba da ciwa al´umar wannan ƙasa tuwo a ƙwarya."

Wani dattijo dake cikin jama´ar da ke bukin zagayowar wannan rana fushi ya yi da cewa.

"Shekara guda ta wuce amma ba abin da ya faru. Babu tsaro, ba zaka iya zuwa arewacin ƙasar ba inda Sabiyawa ke iko. Kuma gwamnatinmu ba ta cika alkawuran da ta yi mana ba."

To sai dai ba haka abin ya ke a dukkan ɓangarorin ƙasar ba. Domin ƙasar ta samu kundin tsarin mulkinta hukumomin leƙen asiri da dakarun tsaron ƙasa da sabbin ma´aikatu da dama masu muhimmanci ga kuma ofisoshin jakadanci. Hakazalika tana samun tallafi daga ƙasashen duniya musamman na kuɗi. A kwanakin nan gwamnatin Kosovo ta yi ta nuni da abubuwan da ta cimma a cikin shekara guda. Ƙasar dai ba za ta iya ci-gaba da samun taimako daga ƙetare don tafiyar da ayyukanta ba.

Duk da cewa matsalar talauci ta yi mata katutu haɗe da taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin masu zuba jari daga ƙetare, gwamnatin Kosovo dai ta gudanar da bukukuwan cika shekara guda da samun ´yancinta. Duk da ƙoƙarin rage hauhawa tsamari da Sabiya tsiraru dake arewacin ƙasar har yanzu da sauran aiki gaba, domin wasu ´yan majalisa daga birnin Belgrade yanzu haka sun shirya wani zaman majalisa na musamman da ´yan siyasan Sabiyawan Kosovo abin da ke nuni da cewa har yanzu suna ɗaukar wannan yanki a matsayin wani lardi na Sabiya.

Sauti da bidiyo akan labarin