Shawarwarin sulhu a game da rikicin Lebanon
May 27, 2007Talla
ƙungiyoyin Palasdinawa na cigaba da shawarwari domin kawo ƙarshen musayar wuta tsakanin sojojin Lebanon da ƙungiyar yan kishin Islama, waɗanda aka yiwa ƙofar rago a wani sansanin yan gudun hijirar Palasdinawan dake Nahr al-Bared a ƙasar Lebanon. Rahotanni sun ce ƙungiyar Fatah ta shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas da kuma ƙungiyar Hamas na daga cikin rukunin ƙungiyoyi dake gudanar da waɗannan shawarwari. A yanzu dai alámura sun ɗan lafa a sansanin bayan ɗauki ba daɗi tsakanin ƙungiyar yan kishin Islaman ta Fatah al Islam da kuma dakarun sojin Lebanon, abin da ya yi sanadiyar mutuwar a ƙalla mutane fiye da 70.