Shawarwarin samar da zaman lafiya a arewacin Uganda | Siyasa | DW | 07.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shawarwarin samar da zaman lafiya a arewacin Uganda

A wani mataki na bazata kungiyar ´yan tawaye ta Lord´s Resistance Army ta yi shailar tsagaita wuta.

Sansanin ´yan gudun hijira a Gulu arewacin Uganda

Sansanin ´yan gudun hijira a Gulu arewacin Uganda

Mummunan yakin basasan na arewacin kasar ta Uganda yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane, ci da gumin kananan yara kuma ana tilasta musu shiga aikin soja. Wakilan MDD sun bayyana wannan yakin basasa da aka shafe shekaru 20 ana yi da cewa shi ne wani bala´i mafi muni da ya shafi dan Adam a duniya baki daya. Kungiyar Lord´s Resistance Army, LRA karkashin madugun ´yan tawaye Joseph Kony ta aikata ta´asa iri dabam dabam, inda ta rika farma kauyuka tana yiwa mutane kisan gilla, ko yanke musu labba da kunnuwa da wasu sassa na jikinsu. Ba dai wanda ya san manufarta ta siyasa face abin da tas a a gaba shine kifar da gwamnatin Uganda.

Amma yanzu shawarwarin samar da zaman lafiya tsakanin manyan jami´an gwamnati da ´yan tawayen LRA zai kawo karshen wannan rikici. Wani kakakin gwamnatin Uganda yayi kyakkyawan fatan cewa da akwai yiwuwar cimma yarjejeniya.

Ya ce: “Ina tsammanin muna da muhimmin aiki a gaban mu. Tuni an kammala matakin farko wanda ke da muhimmanci. Yanzu zamu fara tattaunawa game da kawo karshen fadan da kuma tsagaita wuta. Bayan haka zamu tattauna akan batutuwan da suka shafi shigar da ´yan tawaye a cikin gwamnati da dai sauransu. Yanzu dai mun kai wani matsayi na kwantar da kurar rikicin.”

A cikin wata sanarwa da kakakin sa ya bayar a karshen makon jiya, ba zato ba tsammani madugun ´yan tawaye mista Kony ya yi shailar tsagaita wuta, inda ya ce sun daina kaiwa sojojin Uganda hari. To sai dai a lokutan baya ma kungiyar ta LRA ta sha daukar irin wadannan alkawura amma ba ta cikawa.

Ya ce “Muna takatsantsan domin mun taba fuskantar irin haka, inda aka yi shailar dakatar da yaki amma aka karyata. Yanzu dai zamu yi kokrain ganin mun cimma wata yarjejeniya wadda za´a iya kulawa da ita kuma a aiwatar da ka´idojinta.”

Wata matsala da za´a iya fuskanta a gun shawarwarin shine shugabannin ´yan tawayen kansu ba sa halartar taron na Sudan. Sun tura wakilansu ne, saboda kotun kasa da kasa dake birnin The Hague na neman madugun ´yan tawaye Jaoseph Kony da wasu shugabannin LRA su 3 bisa tuhumar aikata laifukan yaki. Saboda haka za´a samu jinkiri kafin a cimma wata masalaha a wannan taro. To amma duk da haka gwamnatin Uganda na fatan cewa ba za´a dauki fiye da makonni 5 kafin cimma tudun dafawa ba.

Ga mazauna arewacin Uganda hakan na nufin karshen wani mawuyacin hali da suka shafe shekaru 20 suna ciki. Kuma mutane kimanin 1.6 da a halin yanzu suka nemi mafaka a sansanonin ´yan gudun hijira zasu iya komawa kauyukansu.
 • Kwanan wata 07.08.2006
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btym
 • Kwanan wata 07.08.2006
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btym