Shawarwarin maido da danganta tsakanin Amurka da Koriya ta arewa | Labarai | DW | 06.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shawarwarin maido da danganta tsakanin Amurka da Koriya ta arewa

Amurka da Koriya ta arewa na cigaba da tattauanwa a ƙokarin farfaɗo da hulɗar dangantaka a tsakanin su wadda ta yi tsami kusan shekaru 50 da suka wuce. Matainamkin sakataren harkokin waje Amurka Chirstopher Hill da takwaran sa na Koriya ta arewa Kim Kye-Gwan sun isa birnin New York domin tattaunawar. Ƙokarin maido da hulda a tsakanin ƙasashen biyu ta biyo baya yarjejeniyar da aka cimma ne a ranar 13 ga watan Fabrairu a taron ƙasashe shidda wanda ya gudana a Beijin na dakatar da shirin nukiliyar Koriya ta arewa. Kakakin fadar white House Sean McCormack yace Amurka na nazarin cire Koriya ta arewa a jadawalin ƙasashe masu ɗaurewa taáddanci gindi