1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarwarin kulla babbar gwamnatin kawance a nan Jamus

Mohammad Nasiru AwalOctober 28, 2005

A jiya aka gudanar da zagaye na uku na shawarwarin a birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/Bu4X
Zauren taro tsakanin CDU/CSU da SPD
Zauren taro tsakanin CDU/CSU da SPDHoto: AP

Yanzu haka dai ana kara samun ci-gaba a shawarwarin kafa gwamnatin kawance tsakanin jam´iyun Christian Union na CDU/CSU da kuma SPD. A jiya da daddare manyan shugabannin bangarorin biyu suka gudanar da zagaye na 3 a shawarwarin inda suka tattauna akan sakamakon da aka samu kawo yanzu.

Ko da yake shugaban SPD kuma mataimakin shugaban gwamnati mai jiran gado Franz Müntefering ya yi korafi game da tafiyar hawainiya da ake fuskanta a shawarwarin musamman bisa la´akari da cewa wakilan sabuwar gwamnatin hadin guiwar na son cimma wata yarjejeniya gabanin babban taron jam´iyar a tsakiyar watan nuwanba, to amma duk da haka an cimma wani tudun dafawa bisa manufa, kamar yadda shugabar gwamnati mai jiran gado Angeler Merkel ta nunar.

“Na yi maraba da cewar jam´iyar SPD da ta ´yan Christian Union sun cimma yarjejeniya game da ci-gaba da tafiyar da aikin bautawa kasa a fannin soji, da kuma shirin da aka nuna na sake yin nazari akan batun yaki da ta´addanci, musamman dangane da amfani da dakarun Jamus don tinkarar duk wata barazana a cikin gida.”

Jam´iyun dai na kuma yinnazari akan kara yawan shekarun yin fensho zuwa shekaru 67 na haihuwa. To amma sai a shekara ta 2007 zuwa 2008 za´a yanke shawara akan daukar wannan mataki, inji Müntefering. To sai dai shugaban na SPD ya ce a badi ba za´a yiwa ´yan fenshon karin ko sisi kwabo ba. Sannan jam´iyar SPD na tunanin kirkiro wani tsarin haraji na musamman wato kamar karin harajin albashi don magance matsalolin gibin kasafin kudi da suka zamowa kasar kayar kifi a wuya.

Ko wannan tsarin za´a dauka ko kuma wanda jam´iyar Christian Union ke goyawa baya wato karin harajin kayan alatu, abin da ke a fili dai shine dole jama´a ta yi shirin biyan karin haraji. Batun da ake takaddama akai har yanzu shine dangane da manufofin kiwon lafiya inji shugaban na SPD sannan sai ya kara da cewa.

“Har yanzu ba wata kusantar juna a fannin inshora. Shi yasa za´a ci-gaba da shawarwari don samun wata mafita mafi a´ala gare mu baki daya.”

A lokacin yakin nema zabe jam´iyar SPD ta yi suka ga shawarar da Merkel ta abyar game da kirkiro wani tsarin inshorar lafiya na bai daya ba tare da la´akari da yawan albashin ma´aikaci ba yayin da ita kuma jam´iyar SPD ta dage akan wani tsarin da ta kira inshorar jama´a na daidai ruwa daidai tsaki.

An kuma ga alamun cimma daidaito a fannin samar da makamashi ta hanyoyin da ba sa gurbata yanayi.