1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shawarwarin kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa a Jamus

An shiga zagaye na karshe a shawarwarin kafa gwamnatin hadin gwiwa a nan Jamus tsakanin Jamiyun Social Democrats dana Conservatives. Bangarorin biyu na fatan cimma yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnatin a cikin wannan makon. A ranar Litinin bangarorin biyu suka amince da kara waádin shekarun barin aiki daga shekara 65 zuwa 67. Shugaban jamiíyar CDU Volker Kauder yace zaá aiwatar da shirin ne daki daki daga shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2030. Sauran batutuwan da Jamíyun ke muhawara akai sun hada da manufofin gwamnati na cikin gida dana kasashen ketare da kuma yadda zaá shawo kan matsalar gibin kasafin kudi. A game da manufar kasafin kudi, jamíyar Social democrats na mai raáyin kara yawan kudin haraji ga masu samun kudade shiga masu yawa yayin da a daya hannun kuma zaá rage haraji akan kayayyakin bukatu na amfanin yau da kullum.