Shawarwarin kafa gwamnatin hadin gwiwa a Jamus | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shawarwarin kafa gwamnatin hadin gwiwa a Jamus

An shiga zagaye na karshe a shawarwarin kafa gwamnatin hadin gwiwa a nan Jamus tsakanin Jam´iyun Social Democrats da na Conservatives. Bangarorin biyu na fatan cimma yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnatin a cikin wannan makon. A ranar Litinin bangarorin biyu sun amince da kara wa´adin shekarun barin aiki daga shekara 65 zuwa 67. Shugaban jam´iyar CDU Volker Kauder yace za´a aiwatar da shirin ne daki daki daga shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2030. Sauran batutuwan da Jam´iyun ke muhawwara akai sun hada da manufofin gwamnati na cikin gida da na kasashen ketare da kuma yadda za´a shawo kan matsalar gibin kasafin kudi. A game da manufar kasafin kudi, jam´iyar SPD na mai ra´ayin kara yawan kudin haraji ga masu samun kudaden shiga masu yawa yayin da a daya hannun kuma za´a rage haraji akan kayayyakin bukatu na amfanin yau da kullum. Wakilan sassan biyu sun ce har yanzu ba´a cimma tudun dafawa ba game da yiwa manufar kiwon lafiya kwaskwarima.