1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shawarwarin Iran da hukumar IAEA

August 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuDU

Jamián gwamnatin Iran da yan hukumar majalisar ɗinkin duniya mai kula da hana yaɗuwar makaman nukiliya IAEA sun yi tattaunawa ta biyu a birnin Tehran da nufin shawo kan taƙaddamar shirin nukiliyar Iran ɗin. A watan Yunin da ya gabata Iran ta amince zata tsara wani jadawali cikin kwanaki 60 domin buɗe ƙarin ƙofofi ga jamián bincike don nazarin tashar nukiliyar. Jamián Iran ɗin sun baiyana tattaunawar da aka yi a baya da cewa sun yi armashi. Ƙasashe da dama na yammacin turai na zargin Iran da yunkurin mallakar ƙare dangi. A hannu guda dai Amurka ta baiyana yarjejeniyar ta baya bayan nan da cewa abin ƙarfafa gwiwa ne amma dai basu wadatar ba.