1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarar Ministan Cikin Gida Na Jamus Game Da Sansanin 'yan Gudun Hijira A Arewacin Afurka

September 30, 2004

Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun yi kakkausan suka akan shawarar da ministan cikin gida na Jamus Otto Schily ya bayar a game da gina sansanonin 'yan gudun hijira a arewacin Afurka

https://p.dw.com/p/Bvg6
Ministan cikin gida Otto Schily
Ministan cikin gida Otto SchilyHoto: AP

A dai jiya laraba ministan cikin gida Otto Schily ya kara jaddada shawarar tasa game da bude sansanonin karbar ‚yan gudun hijira dake neman shigowa nahiyar Turai domin neman mafakar siyasa, a can arewacin Afurka, inda yake cewar:

A hakika dai duk wanda ya lura da mawuyacin halin da ake ciki a yankin tekun bahar rum zai fahimci muhimmancin dake akwai wajen neman bakin zaren warware wannan matsala. Domin kuwa ba zata yiwu a zura ido ana kallon yadda rayukan mutane ke salwanta ba tare da an tabuka kome ba. Sannan a daya bangaren kuma wajibi ne a kawo karshen tuttudowar dubban daruruwan ‚yan gudun hijirar dake bi ta tekun bahar rum domin shigowa nahiyar Turai.

Wannan shawarar ta Schily dai tana samun goyan baya daga Birtaniya da kuma sabon kantoman shari’a na kasashen Turai da za a nada nan gaba, amma Faransa da Sweden sun ce ba su da hannu a wannan batu daidai da wasu kungiyoyin kare hakkin dan-Adam. Domin kuwa wannan sansanin ba zai taimaka a hana tuttudowar ‚yan gudun hijirar ba a cewar Wolfgang Grenz daga kungiyar neman afuwa ta Amnesty International. Duk wanda bai samu nasarar amincewa da takardunsa na neman mafakar siyasa a wannan sansani ba zai sake wata sabuwar harama ta satar hanyar shigowa nahiyar Turai ta kan tekun bahar rum. Bugu da kari kuma ko da mai neman mafakar siyasar ya samu amincewa da takardunsa hakan ba ya nufin cewar za a ba shi damar kutsawa wata kasa ta Kungiyar Tarayyar Turai kai tsaye. Domin kuwa, a karkashin shawarar ta Schily, su kansu kasashen ne ke da ikon yanke shawarar karbar ‚yan gudun hijirar a wawware. A lokacin da yake bayyana ra’ayinsa game da wannan batu Volker Beck kwararren masanin al’amuran cikin gida na jam’iyyar The Greens cewa yayi:

A gani na babu wani dalili ga KTT da ta kafa irin wannan sansani a arewacin Afurka. Domin kuwa hukumar ‚yan gudun hijira ta MDD tuni ta giggina sansanonin karbar ‚yan gudun hijira a duk wani yankin da ake fama da rikici a cikinsa, kuma ana iya sassauta matsalar idan kowace kasa ta KTT zata tsayar da shawarar karbar wani kaso na ‚yan gudun hijirar daga wadannan yankuna.

Kungiyar Amnesty tayi kira ga ministocin cikin gida na kasashen KTT da su yi gyara ga kudurin da suka gabatar game da karbar ‚yan gudun hijira a cikin watan afrilun da ya gabata domin kuwa yawa-yawancin kasashen da ake neman kafa irin wannan sansani a cikinsu kamar dai Libiya ba su da wata sahihiyar doka dake girmama hakkin makaurata.