Shawarar haramta niƙabi a Faransa | Siyasa | DW | 27.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shawarar haramta niƙabi a Faransa

Wani kwamiti da ya ƙunshi jam'iyu da dama da majalisar dokokin Faransa ta naɗa, ya gabatar da shawarwari kan matakan haramta niƙabi gaba ɗaya a wurare na gwamnati da motocin bas a ƙasar

default

Kwamitin da ya ƙunshi wakilai 32 a cikin sa, yace wajibi ne a tilastawa mata a Faransa ɗin su dakatar da amfani da duk wani abin da zai rufe fuskoki da jikin su gaba ɗaya a wurare mallakar hukuma, kamar asibitoci da motoci na suhuri. Rahoton ya kuma nemi majalisar dokokin ta Faransa ta gabatar da dokoki game da haka ba tare da wani jikiri ba.

Watanni shidda kwamitin na majalisar dokoki yayi, yana nazari a game da ko ya dace a haramta wa mata musulmi su riƙa amfani da niƙabi, abin dake rufe fuskoki da jikin su gaba ɗaya. Kwamitin ya ƙunshi 'yan siyasa da masana da wakilai na ƙungiyoyin jama'a da addinai a cikin sa. Jaridar mako-mako mai suna le Point ta yi ƙorafin cewar muhawarar da aka yi a kwamitin, bata yi dabam da yadda aka saba gani a Faransa ba, wato tsari na Faransawa ya haɗu da batun kare hakkin mata da  al'amuran siyasa da  zamantakewa. Wakilan kwamitin sun yi nazari a kan dukkanin waɗannan al'amura tsawon watanni bakwai, to amma a ƙarshe babu abin da ya samu in banda rashin daidaituwa, musmaman a game da ko ya dace a haramta amfani da niƙabi ɗin ko kuma  bai dace ba.

Frankreich Schüler auf dem Schulhof in Paris Kopftuch

Mafi yawan masana shari'a suka ce bai dace a haramta niƙabi ɗin ba, domin kuwa ko ma an yi haka, kotun kare tsarin mulki na Faransa ko kotun kare hakkin 'yan Adam ta ƙasashen Turai ɗayan su zai hau kujerar naƙi domin adawa da wannan mataki. Shima wanda ya kafa wannan kwamiti, Andre Gerin, na jam'iyar kwaminis, yace bai dace a haramta niƙabi ba, saboda a  ra'ayin sa.

Matsalar ba ita ce ta neman a hukunta mata ba, amma abin da ake buƙata shine hana   tsattsauran ra'ayi na musulunci da rage ƙarfin masu kiran kansu malaman musulunci suna cusa ra'ayoyi, tare da neman ɓata musulmi da musulunci a Faransa.

Ana kuma samun rashin fahimta a tsakanin su kansu masu ra'ayin 'yan mazan jiya. 'Yan majalisar dokoki da dama daga cikin su sun kasance a kwamitin na bincike, to amma musamman daga ɓangaren shugaban ƙasa, Nicholas Sarkozy da Pirayim minista Laurent Fillon a hannu guda da kuma ɓangaren Jean Francois Cope, shugaban jam'iyar  UMP, wanda ma ake cewa yana burin neman muƙamin shugaban ƙasa.

Tun a lokacin da kwamitin yake nazarin sa, Cope yace zai gabatarwa majalisar dokoi tsarin wata doka da zata haramta wa mata amfani da niƙabi. Inda kuwa babu banbanci na shari'a da na siyasa tsakanin sa da Sarkozy, da sai ace yana faɗin ra'ayin shugaban na Faransa ne kawai, wanda yace:

Frankreich Schüler auf der Straße in Lyon Kopftuch

Faransa ƙasa ce da mata suke da 'yancin su, inda ake mutunta 'yanci da addini kowa. To amma Faransa kuma ƙasa ce da niƙabi bashi da wuri a cikin ta. Faransa ba ƙasa ce inda za'a riƙa take hakkin mata ba ta ko wace hanya.

Kwamitin ya gabatar da shawarwari guda ashirin a game da batun na niƙabi. Da farko an baiwa 'yan majalisar dokokin na Faransa wa'adin watanni shidda, su ja hankalin mata masu sanya niƙabi ya zuwa ga rashin dacewar wannan mataki, misali ta hanyar Allah wadai da shi a majalisar, su kuma amince da doka a majalisar da zata haramta  amfani da niƙabi a wurare mallakar hukuma, kamar asibitoci, makarantu da ofisoshin gwamnati.

A kwamitin, wakilai na ƙungiyoyin musulmi gaba ɗaya sun nuna cewar niƙabi ba abu ne da musulunci ya tilasta shi a kan masu addinin ba. To amma duk da haka, ana ɗaukar cewar muhawara game da haramta niƙabi ɗin wani kampe ne na adawa da musulmi.

Mawallafa: Johannes Duchrow/Umaru Aliyu

Edita: Mohammed Nasiru Awal