1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarar Canza Bikin Uku Ga Watan Oktoba

November 4, 2004

Gwamnati na shawarar canza ranar bikin sake hadewar Jamus daga uku ga watan oktoban kowace shekara zuwa ranakun lahadi na farkon wannan wata, lamarin dake fuskantar mummunar adawa a duk fadin kasar

https://p.dw.com/p/Bvet

Ba dai tare da wata rufa-rufa ba, ministan tattalin arzikin Jamus Wolfgang Clement ya fito fili yana mai bayyana cewar, wannan ba wani ra’ayi ne da gwamnati ke shawara kansa ba, tuni bakin alkalami ya bushe a game da wannan manufa. Wato dai a takaice gwamnati na da niyyar soke ranar bikin sake hadewar Jamus, a matsayin wata rana ta hutu a kasar tun daga shekara mai zuwa. Dalilinta game da haka kuwa shi ne kasancewar duk wata rana ta hutun da za a soke zata taimaka wajen samun karin kashi 0,1% na bunkasar tattalin arzikin kasa da samarwa da gwamnati karin kusan Euro dubu 500 ga baitul-malinta. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda ‚yan kasuwa suka yi marhabin da wannan shawara, inda shugaban majalisar ciniki ta Jamus Ludwig Georg ke batu a game da wata kyakkyawar alama ta hangen nesa, domin kuwa sai da aiki ne za a samu sabbin guraben aikin yi ga jama’a. Amma fa bisa ga ra’ayin ‚yan hamayya, ko da yake ba ra’ayin gwamnati ne a soke bikin sake hadewar gaba daya ba, illa kawai a canza masa rana zuwa lahadi ta kowane oktoba a shekara, a maimakon hutun ranar uku ga oktoban, wannan manufa ba mai karbuwa ba ce. A lokacin da yake bayani Michael Meister kakakin rukunin Christian Union a majalisar dokoki cewa yayi:

Wannan na nunarwa ne a fili cewar har yau jam’iyyar SPD ba ta dauki hadewar Jamus da muhimmanci ba, kuma har yau ‚yar rakiya ce bata ma ankara da cewar Jamus ta sake hadewa ba. Idan har hakan ta tabbata kama daga shekara mai zuwa to kuwa wajibi ne a nemi bayani daga ministan kudi Hans Eichel a game da ko shin wace rana ta hutu ce kuma yake fatan ganin an soketa a shekara ta 2006 domin cike gibin kasafin kudin da gwamnatinsa ke fama da shi.

An fuskanci suka da kakkausan harshe daga jihar Bavariya, inda aka kwatanta manufar tamkar abin kunya ga gwamnati. An saurara daga bakin Günter Nooke wakilin CDU a majalisar dokoki yana mai batu a game da wani yunkuri na cin amanar kasa idan har gwamnati tayi kurarin soke wannan rana ta bikin sake hadewar Jamus. Shi ma gwamnan jihar Thuringiya Dieter Althaus dan jam’iyyar CDU ya gabatar da kira ga gwamnati da ta rika yin sara tana duban bakin gatarinta, domin kuwa babu wata kasa ta duniyar nan ta mu da zata yarda ta sa kafa tayi fatali da irin wannan ranar dake da muhimmanci a cikin tarihinta. Hatta wasu daga cikin jami’an the Greens dake hadin guiwa da SPD sun soki lamirin wannan shawara, inda suka ce gwamnati ba zata iya yin gaban kanta wajen yanke wannan kuduri ba tilas ne ta nemi amincewar ‚yan hamayya. Idan har an mayar da bikin zuwa lahadi to kuwa za a wayi gari bikin ya fada ranar 7 ga watan oktoba a shekara ta 2007, wacce zata yi kacibis da ranar bikin kafa tsofuwar JTG a shekara ta 1949.