Sharuɗan janye yajin aikin Afirka ta kudu | Labarai | DW | 31.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sharuɗan janye yajin aikin Afirka ta kudu

Kungiyoyin kodagon Afirka ta kudu sun lashi takobin ci gaba da yajin aiki matiƙar gwamanti ta ƙi biya musu bukatunsu.

default

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon Afirka ta kudu ta yi watsi da tayin ƙarin kashi 7.5% na albashi da gwamanti ta yi mata, domin ta kawo ƙarshen yajin aikin da ta fara makwani ukun da suka gabata. Ɗaya daga cikin shugabannin COSATU wato Mugwema Nkwamba ya shaidawa kanfanin dillacin labaran Faransa cewa, matikar yawan kuɗin bai kai kashi 8.6% kamar yadda suka bukata ba, to zasu ci gaba da gudanar da yajin aikin.

Ɓangarorin biyu sun amince da komawa kan teburin tattaunawa domin ci gaba da nazarin bukatun ma'aikatan ƙasar ta Afirka ta kudu da yawansu ya kai miliyon ɗaya da kuma dubu 300. Shugaba Jacob zuma ya umurci ministocin da alhakin ya rataya musu a wuya da su hanzarta kawo ƙarshen yajin aikin da ke iya yaɗuwa zuwa ga masana'antun hako ma'adinai.

Ya zuwa yanyu dai, asibitoci da kuma makarantu na daga cikin wuraren da yajin aikin ya fi gurgantawa a ƙasar ta Afirka ta kudu. Sojoji 4.000 gwamnati ta tura domin gudanar da ayyukan jiyya a asibitoci 58 na ƙasar ta Afirka ta kudu.

Maawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu