Sharon zai ci-gaba da zama cikin suman da aka sa shi har zuwa gobe | Labarai | DW | 08.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sharon zai ci-gaba da zama cikin suman da aka sa shi har zuwa gobe

Har yanzu FM Isra´ila Ariel Sharon na cikin mummunan hali na rai kwakwai mutu kwakwai kwanaki hudu bayan ya kamu da matsananciyar mutuwar jiki. A halin da ake ciki likitocin da ke masa magani sun ce zasu kyale shi a cikin sumar da suka sa shi har zuwa gobe litinin. Gidan radiyon Isra´ila ya rawaito majiyoyin kiwon lafiya na cewa likitocin sun yanke wannan shawarar ne bayan sun yi nazarin hoton kwakwalwarsa da aka dauka da sanyin safiyar yau lahadi. Yanzu haka dai likitocin na da kyakkyawan fatan cewa zasu iaa ceto ran FM mai shekaru 77 da haihuwa, to amma sun yi kashedin cewar halin da ya ke ciki ba zai ba shi damar ci-gaba da daukar nauyin tafiyar da al´amuran mulki a kasar ta Bani Yahudu ba. Likitoci a asibitin Hadassah dake Birnin Kudus sun gano raguwar kumburin da kwakwalwar Sharon ta yi bayan tiyata ta gaggawa har sau 3 da aka yi masa.