Sharon ya sake shiga mummuan hali na rashin lafiya | Labarai | DW | 11.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sharon ya sake shiga mummuan hali na rashin lafiya

Likitoci dake yiwa FM Isra´ila Ariel Sharon magani sun fara yi masa aikin tiyata na gaggawa a kan cikinsa. Likitocin suka ce rayuwar Sharon na cikin wani mummunan hadari. A cikin makonnin da suka wuce Sharon ya dan fara farfadowa daga sumar da aka sa shi bayan yayi fama da matsanancin bugun jini a ranar 4 ga watan janeru. Kakakin asibitin da aka kwantar da shi a birnin Kudus ya ce sabon hoton da aka dauka na cikin FM ya nuna wani mummunan lahani. Saboda haka yanzu kwararrun likitocin fida sun fara masa tiyata da zata dauki kimanin sa´o´i 3 zuwa 6. yanzu haka saura makonni 6 a gudanar da zaben ´yan majalisar dokokin Isra´ila a ranar 28 ga watan maris. Tun lokacin da aka kwantar da shi mataimakinsa wato Ehud Olmert ke tafiyar da aikin FM na rikon kwarya.