Sharon ya fito daga dakin tiyata | Labarai | DW | 06.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sharon ya fito daga dakin tiyata

Likitoci a asibitin Hadassa dake birnin Qudus,sunce sun dakatar da jini dake kwarara a kawnyar prime ministan Israila Ariel Sharon bayan tiyatar gaggawa a yau .

Darektan asibitin Shlomo Yosef,yace bayan tiyatar na saoi 5 sun kawshe jin da ya zuba,kodayake darektan bai naiyana ko zasu farfado da Sharon daga allurar suma da sukayi masa domin duba irin halin da yake ciki.

A yau din nan ne aka sake mayarda Sharon dakin tiyata karo na uku cikin saoi 48,bayan bincike da ya gano har yanzu jini na zuba cikin kwakwalwarsa,bayan tiyata na saoi 7 da akayi jiya alhamis.