Shari´ar ´yar adawa ta Burma San Suu Kyi | Siyasa | DW | 18.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari´ar ´yar adawa ta Burma San Suu Kyi

An sake ɗage shari'ar 'yar adawa ta Burma Aung San Suu Kyi zuwa gobe Talata bayan sa'o'i kaɗan na sauraron ƙarar da aka shigar game da ita.

default

Aung San Suu Kyi shugabar ´yan adawa ta Burma

Hukumomin ƙasar na zarginta ne da laifin keta dokar ɗaurin Talala da aka yi mata, bayan wani Ba Amurke ya kai mata ziyara. Yanzu haka dai wannan mata tana fuskantar ɗaurin shekaru biyar muddin dai an kama ta da wannan laifi.

An yi shari'ar ta yau ne cikin tsauraran matakan tsaro, an rufe dukkanin tituna dake kan hanyar zuwa babban gidan yarin ƙasar, a birnin Rangoon.

Jami'an tsaro cikin rigar sarki ne suka hana jama'a ratsawa ta waɗannan hanyoyi. Waɗanda suka ganewa idonsu sun ga Aung San Suu Kyi da lauyanta da kuma wani jami'in ofishin jakadancin Amurka sun shiga kotun, saboda ana zargin Ba Amurke da ya kai mata ziyara.

Jakadu huɗu na ƙasashen Jamus da Faransa da Burtaniya da kuma Italiya sun nemi shiga kotun domin halartar wannan shari'a da aka gudanar a asirce, sai dai kuma jami'an tsaron sun hana su wucewa.

Dubban 'yan ƙasar Burma da ke zaman mafaka a ƙasashen kudu maso gabacin Asiya sun fito zanga zanga suna masu nuna adawarsu da wannan shari'a. Haka bakin ofishin jakadancin Burma a birnin Bangkok na ƙasar Thailand masu zanga zanga sun yi kira da a saki Aung San Suu Kyi. Wasu sun sanya kayayyaki irin na sojin Burma ɗauke da bindigogin wasa na roba. Wata matashiya kuma sanye da kaya irin na Aung San Su Kyi tana ɗaure cikin wani keji. Masu zanga zangar dai suna masu kira ga ƙasashen duniya da su matsawa gwamnatin Burma lamba game da wannan mata.

Wasu 'yan gudun hijira na Burma sun sanar da sake yin wata zanga zangar a cikin ƙasar muddin dai an yanke hukuncin ɗaure ta a gidan yari.

"Idan har gwamnatin mulkin sojin ba ta saki Aung San Suu Kyi ba, ba anan ba kaɗai a ko-ina cikin duniya mutane zasu bazu kan tituna suna masu nuna adawarsu har ma da cikin Burma kanta, dole ne a sake ta kuma a samu kafuwar demokuraɗiyya a ƙasar mu."

Majiyoyin sojin ƙasar dai sun ce an dakatar da shari'ar har zuwa gobe. Kafin ya shiga kotun a yau lauyanta yace tana nan kan bakanta kuma bata nuna wani tsoro ba. Majiyoyi daga kotun kuma sun ce Aung San Suu Kyi wadda ta samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, ta haƙiƙance cikin kotun cewa dole ne a kira ta da sunanta na yanka. Mahaifinta dai wani gwarzo ne a ƙasar Aung San. Sai dai alƙalin ya ci gaba da kiranta da Suu Kyi.

Mawallafa: Bernd Musch-Borowska / Hauwa Abubakar Ajeje

Edita: Mohammad Nasiru Awal