1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar yan ta´ada a kasar Belgium

February 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7o

Wata kotu a birnin Bruxellles na kasar Belgium, ta kammalla shariar mutane 3 daga jimmilar mutane 13 da ta ke tsare da su wanda kuma a ke zargi da hannu acikiharen ta´anadamnci Casablaka na kasar Marroco, da na Madrid.

Idan ba a manta ba, a watan mayu ne, na shekara ta 2003, wasu yan takife, su ka kai hari, a birnin Madrid na Spain, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 191, da kuma Casablanca a kasar Marroco , a shekara ta 2004,inda mutane 33 su ka rasa rayuka.

Kotun, ta sami wannan mutane 3, da hannu a cikin bada masauki ga wasu membobin kungiyar GICM ta kasar Marroco mai alaka da Alqa´ida wada kuma ta kitsa hare haren Casablanca da na Madrid.

Dukan mutanen 3 wato Abdelkader Hakimi, Lahussine El Haski da Mustafa Lunani,sun hito daga Marroco, amma sun jimma kasar Belgium.a matsayin yan ci rani