1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar tsofan shugaban kasar Rwanda a birnin Kigali

November 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvIl

A birnin Kigali na Rwanda,yau ne kotun koli, ta koma sharia´r sauraran daga kara, da tsofan shugaban kasar Rwanda, Pasteur Bizimangu ya gabatar a gaban ta.

Tun watan Aprul ne shekara ta 2002 kotu, ta yanke hukuncin daurin shekaru 15 a kurkuku, ga tsofan shugaban, bayan an same sa, da hannu dumu dumu, a cikin kisan kiyasun da ya wakana a kasar.

Pasteur Bizimangu ya gurfana, tare da tsofan misintan sa, na zirga zirga da sauran mutane 6.

Lauyoyin tsofan shugaban, sun bayyana cewa, hukunci da a ka yanke masu da farko, ba a yi sa ba cikin adalci.

Pasteur Bizimangu ya jagoranci Rwanda daga shekara ta 1994 zuwa 2000.

A daya hannun, kotun mussaman ta kasar Rwanda, mai sharia´ar leffikan yaki, ta tuhumi tsofan ministan kasuwanci na kasar da yayi kasa ko bisa a kasar Belgium da massaniya a game da kissan kiyasun da ya wakana a Rwanda, a shekara ta 1994.