Shari´ar tsofan shugaban ƙasar Irak
April 19, 2006Talla
A ƙasar Irak, yau za a zama na 22 ,a shari´ar tsofan shuganan ƙasa Saddam Hussain.
A zaman ranar litinin da ta wuce, ƙurrarun massana sun tabbatar da cewa, takardar da ta bada izinin hallaka yan shi´a 148, a garin Dujail tun shekara ta 1982, na ɗauke da sa hannun Saddam Hussain.
Saidai lauyoyin tsofan shugaban, sunyi watsi da wannan sakamako.
A game da haka, babban alƙali, ya bada ƙarin kwanaki 2, domin tabatar da ko sa hannun na Saddam Hussain ne, ko kuma a´a.
Lauyoyin Saddam, sun bukaci samar da ƙurraru daga ƙetare, domin gudanar da wannan bincike, ta la´akari da wanda ke yin sa a yanzu, na da alaka da gwamnatin ƙasar Irak.