1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari'ar Taylor

A yau ne ake ci gaba da sauraron shari’ar tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun lefuka dake birnin Hague ƙasar Holland.Wani kƙwararre akan cinikin dimonti da ake kwasa a matsayi ganima shine farkon wanda ya ba da sheda a shari’ar ta yau bayan an dakatad da ita watanni shida da suka gabata.Ya faɗa wa kotun cewa dimonti ne ya ƙara rura wuta a ƙasar sSaliyo.Ana tuhumar Taylor ne da laifin jagorantar yan tawayen Saliyo da su ka yi ƙaurin suna wajen daddatsa gaɓoɓin mutane a yaƙin basasan ƙasar na shekaru 10. Ana zargen shi da aikata lefuka da su ka haɗa da kisa, fyaɗe, bautar da yara kanana da kuma basu horo na aikin soja.