Shari′ar Taylor | Siyasa | DW | 04.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari'ar Taylor

A yau litinin ake gabatar da shari'ar tsofon shugaban Liberia Charles Taylor a kotun kasa da kasa dake the Hague

Charles Taylor

Charles Taylor

Shi dai tsofon shugaban Liberiya Charles Taylor ya musunta dukkan zargin da ake yi masa na daukar matakai na rashin imani da gallaza wa talakawa da dai ta’asa iri daban-daban da ba a taba ganin irin shigensa ba a yake-yaken basasar Afurka, inda yake cewar:

“Ko sau daya ban taba zub da jinin al’uma ta domin in arzuta kaina da kai na ba, kuma ba zan taba yin hakan ba.”

Amma babban mai daukaka kara Stephen Rapp da ita kanta kotun kasa da kasa dake birnin The Hague, basu da wanannan ra’ayi na Charles Taylor. Domin kuwa a ganinsu Charles Taylor mai shekaru 59 da haifuwa ba kawai ya zub da jini ne a kasarsa ta Liberiya ba, kazalika har da makobciyar kasa ta Saliyo. Charles Taylor ya taimaka wa tsofon madugun ‘yan tawayen Saliyo marigayi Foday Sankoh da makamai da sojan haya a madadin tukwici da diamenti. Kafin a dora hannu kan kudadensa na ajiya Charles Taylor ya tara abin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu da dari biyar a kasar Switzerland. ‘Yan tawayen da Taylor ke goya musu baya a Saliyo sun yi amfani na sojoji yara a yake-yakensu kuma har yau akasarin al’umar saliyo da aka daddatse gabobinsu suna fama da wani mummunan hali na gigin barci. A yakin basasar na Saliyo an kashe mutane sama da dubu dari da asdhirin a baya ga fyaden da aka yi wa kusan kashi 70% na mata a kasar. Kafin rikicin na Saliyo Taylor ya fafata kazamin yakin basasa a Liberiya, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane dubu 250, wato kwatankwacin kashi goma cikin dari na illahirin al’umar kasar. Taylor ya dare kan karagar mulki sakamakon zaben da al’umar liberiya suka yi don neman zaman lafiya, kafin a fatattake shi daga kasar a shekara ta 2003. A cikin jawabinsa na ban kwana da yayi a wancan lokaci Taylor cewa yayi:

“Tarihi dai ya nufe ni da alheri. Na cimma burina na biya wa al’umar liberiya bukatunsu. Shugabanci ba ya da muhimmanci. Ko shakka babu muna iya ci gaba da fafatawa, amma maganar ta shafi makomar al’umar kasa ne. A saboda haka na amince da rawa ta a matsayin ragon layya.”

Shekaru uku bayan zaman hijira a Nijeriya aka cafke Taylor aka tasa keyarsa zuwa The Hague saboda fargabar yadda al’amura zasu kasance in an gurfanar da shi a Saliyo. A nata bangaren sabuwar shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf tayi bayani game da shari’ar inda ta ce:

“Abun da zan ce shi ne zamu yi bakin kokarinmu wajen ganin an jefar da tarihin Mr. Taylor a kwandon shara. Ba abin da muke bukata illa mu ga an kawo karshen lamarin. Muhimmin abin dake gabanmu shi ne sulhu da hadin kai don sake gina kasarmu.”

Shari’ar dai zata duba rawar da Taylor ya taka ne a siyasance da kuma irin alhakin dake kansa a yakin basasar da aka yi tsawon shekaru da dama ana fafatawa, in ji Wener Korte, kwararren masani akan al’amuran Liberiya.