Shari′ar Saddam Hussein | Siyasa | DW | 22.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari'ar Saddam Hussein

Ko da yake babu wata takamaimiyar rana da aka tsayar, amma tuni aka kammala shirye-shiryen gabatar da shari'a akan tsofon shugaban kasar Iraki Saddam Hussein

An ragargaza mutum-mutunin Saddam Hussein bayan mamayae Bagadaza a watan maris na 2003

An ragargaza mutum-mutunin Saddam Hussein bayan mamayae Bagadaza a watan maris na 2003

Wani kundin doka da aka dade ana gudanar da aiki kansa a asurce shi ne zai zama shimfidar shari’ar akan Saddam Hussein. To sai dai kuma kwararrun masana al’amuran doka a kasashen ketare tuni suka fara gargadi a game da ba wa shari’ar wani fasali na neman ramuwar gayya, a maimakon a tafiyar da ita tsakani da Allah, ba tare da sauraren shaidar zul ba. A sakamakon haka suke matsin lamba wajen ganin lalle sai an mika tsofon shugaban kasar Irakin dake tsare a Tikrit tun sha uku ga watan desamban bara zuwa ga hannun kotun duniya dake birnin The Hague domin fuskantar shari’a a can. Amma a cikin wani bayani da ya bayar a birnin Bagadaza Muwaffak el Rubai daga majalisar mulkin rikon kwarya ta kasar Irakin ya ce wannan magana ma ba ta taso ba. Ya ce shi da mukarrabansa ba su da ra’ayin cewar kamata yayi Saddam Hussein ya tashi daga Iraki. Za a yi shari’ar ne a bainar jama’a saboda ta haka ne za a tsage gaskiya. Kuma idan zarafi ya kama ana iya nemo kwararrun masana daga Amurka da kasashen Turai da ragowarsu. Duka-duka abin da kotun zata tantance shi ne ta’asa da miyagun laifuka da tsofuwar gwamnatin Iraki ta tafka a cikin mulkinta na sama da shekaru talatin. A tsakanin wannan lokaci an azbtar tare da halaka dubban daruruwa ko kuma ma miliyoyin mutane. Akwai bayanai masu dimbim yawa a game da wadannan miyagun laifuka na keta haddin dan-Adam da suka barbazu a hannun mutane a duk fadin kasar Iraki. Da farko wajibi ne a tara wadannan bayanai kuma ba’ada bayan haka a saurari kararraki daga kasashen Iran da Kuwait, wadanda suka fuskanci hare-hare daga sojojin Saddam Hussein. To sai dai kuma kawo yanzu ba a sanya ranar fara shari’ar ba, sai bayan an kammala shari’ar mukarraban tsofon shugaban na Iraki a jam’iyyar Ba’ath. Da yawa daga Irakawan dai sun harzuka matuka ainun a game da matsayin da Amurka ta ba wa Saddam na kasancewa fursunan yaki. An ji irin wannan bayani daga Entifadh Qanbar daga jam’iyyar Congress ta Iraki, wanda ya ce da zarar an danka Saddam Hussein ga majalisar mulkin Iraki to kuwa ba zata yi wata-wata ba wajen gurfanar da shi gaban kotu domin amsa zargin ta’asar yaki domin ya samu huncin da ya fi dacewa da shi. Doka zata ba shi cikakken ikon kare kansa. Kuma yana da damar daukar lauya ko da kuwa daga ketare ne. A hakika dai ba wanda ya san lokacin da Amurka zata saki fursunan nata na yaki da take fuskantarsa da tambayoyi domin ta danka shi ga majalisar mulkin rikon kwaryar ta kasar Iraki. Akwai mummunan sabani tsakanin kwararru a game da irin hukuncin da za a yanke masa saboda Amurka ta dakatar da hukunce-hukuncen kisa bayan mamayar Bagadaza. To sai dai kuma Muwaffak el Rubai ya ce majalisar mulkin rikon kwarya na da cikakken ikon aiwatar da hukuncin kisan bayan an danka mata ragamar mulki a cikin watan yuni mai zuwa. Ana iya zartar da hukuncin a ranar daya ga watan yuli. Wannan hakki ne na al’umar Iraki, in ji jami’in siyasar.