Shariar Saddam Hussaini | Labarai | DW | 21.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shariar Saddam Hussaini

kashe mutane dari da arbain da takwas a garin Dujail a lokacin mulkinsa.

A zaman na yau mutumin da ya bada bahasi ya bayyana a fili ba kamar a baya bainda masu bada bahasin suka rinka magana da bayan labule,koda ike wasu daga cikin masu bada bahasin sun sake yiwa kotun jawabi ta bayan labule.

A lokacinda kotun take zaman nata Saddam ya bukaci da a dakatar da zaman domin ayi sallar azahar amma alkalin yaki amincewa da hakan wanda hakan yasa Saddam din ya dauki tsawon minti goma yana sallar a kan kujerarsa.

Saddam din dai a zaman na yau yashaidawa kotun cewa sojojin Amurka sun rinka gana masa azaba kuma suka rinka lakada masa duka inda yace har yanzu ma akwai alamar bulalar da suka rinka yimasa a jikin nasa.