Shari´ar Saddam Hussain
November 28, 2005Nan gaba a yau ne, a kasar Iraki kotu za ta fara shari´ar tsofan shugaban kasa Saddam Hussain, tare da 7 daga wasu na hannun damar sa.
Kotu na tuhumar su, da kissan kiyasu a kan mutane 148 a garin Doujail,dake arewanci Bagadaza, tun shekara ta 1982.
Kotunan kasar Iraki, sun bayyana cewa wannan leffi,somin tabi ne daga dimbin leffikan da ake tuhumar tsofan shugaban kasar da aikatawa a zamanin mulkin sa.
Tun ranar 19 ga watan oktober da ta wuce a ka fara wannan shari´a amma a ka dage ta, dalili da rashin yan shaida.
A wannan karro, an tabbatar da cewa, za su hallarci kotun.
Saidai masu kulla da al´ammura a wannan kasa na bayyana cewa akwai alamun a yanzu ma a sake dage shari´ar don gudun karin yaduwar tashe tashen hankulla a yayin da ya rage kawanaki kalilan a gudanar da zaben yan majalisun dokoki.
A bangaren tashe tashen hankulla kam , su na ci gaba da wakana babu kakkabtawa.