Shariar Sadan Hussein A Bagadaza | Siyasa | DW | 19.10.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shariar Sadan Hussein A Bagadaza

default

Acigaba da mayar da martananin alummomin duniya dangane da bude sauraron shariar tsohon Shugaban Iraki Sadam Hussein ayau akasar Iraki,Iran ta bukaci kara yawan laifuffuka da ake zarginsa dasu.

Iran tace tayi maraba da sharian Sadam,amma tana bukatar a kara yawan laifuffuka da ake zarginsa dasu ,bisa ga zargin kisan gillan mutane 140,da sinadrai masu guba.

Kakakin maaikatar harkokin wajen kasar Hamid Reza Asefi,ya bayyana tsohon shugaban Irakin da kasancewar mutumin daya aikata miyagun laifuka ga rayukan biladama.

Sashin Shariar Iran din dai tun a jiya ta aike da nata koke dangane da Sadam,ciki harda kisan gillan da akayi ta hanyar amfani da sinadrai masu guba daga shekarata 1980-1988,alokacin yakin Iran da Irakin.

Tace koken sun hadar da jefawa boma bomai a makarantu,da masallatai da gidaje,wadanda suke dauke da guba,wadanda suka sabawa dokokin kasa da kasa da aka cimma a birnin Hague da kuma Geneva.Bugu da kari Iran tace wadannan hare haren sun sabawa dokokin addinin musulunci,hare harenda suka kasha limamai da mata da kananan yara wadanda basu jib a basu gani ba.

Asefi ya jaddada cewa yakin da Iraki ta kaddamar akan kasashen Iran da Kuwaiti da alummominsu na daga cikin manyan laifuka daya kamata a gabatar alokacin shariar Sadam agaban wannan kotun.

To acan garin kurdawa na Halabja kuwa,wadanda suka tsira daga daga harin guban da Sadam ya aike musu da ita a shekarata 1988,sunyi fata shariar zata kai tsohon shugaban Irakin ga jyanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Daya daga cikin kurdawan Pakhshan Mohammed Hama,wanda ya rasa yayansa guda uku a harin sidaran iskar guban a wancan lokaci,yace matukar Sadam yana raye,to wahalhalunsu basu kare ba.

A ranar 16 ga watan Maris na shekarata 1988 dai kimanin mazauna garin na Halabja dubu 5 suka rasa rayukansu ,sakamakon iskar gas mai guba da aka busawa garin.Kurdawan dai sun zargi gwamnatin sadam Hussein da bada umurnin wannan kisan gillan,domin hukuntasu daga yunkurin neman yancin arewacin Irakin,lokacin yakinta da Iran.

To sai Jagoran alkalai biyar dake shariar Sadam Hussin kuma Bakurde Rizkar Mohammed Aminya dagesauraron karan har zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba.

An dai zartar da dage sauraron karan ne a dangane da bukatar da lauyan wanda ake karan da mukarrabansa ,suka nemi jinkirtawa.

Koda yake Babban alkalin ya danganta dage karan da rashin bayyanan masu bada shaida,wadanda suka ki bayyana saboda tsoro.

Ayayinda tawagar Lauyoyi dake kare sadam Hussein dake da zama a Jordan,suka zargi gwamnatocin Iraki dana Amurka da hana,lauyoyi wadanda bay an kasar iraki bas u gana da hambararren shugaban na Iraki.

 • Kwanan wata 19.10.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4n
 • Kwanan wata 19.10.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4n