1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariar Sadam

Zainab A MohammedApril 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bu72

A yau ne aka cigaba da sauiraron shariar hambararren shugaban Iraki sadam huddein dangane da kisan kiyashi da akayi a kauyukan yan shiaa,koda yake bai bayyana a kotun ba.An dai fara sauraron shariar na yau ne da bayyanan tsohon babban Alkali na kotun juyin juya hali ,a zamanin Sadam, watau Awad Ahmad al-Bandar,shi kadai.An dai kirashi gaban kotun ne ayau domin sake masa tambayoyi,inda daga baya aka dage cigaba da sauraron shariar zuwa 12 ga watan Aprilun da muke ciki.

Awad al-Bandar dai na daya daga cikin mukarraban Sadam guda 7 da ake zarginsu da kisan kiyashin yan shia 148 ,daga kauyen Dujail,bayan yunkurin kashe tsohon shugaban irakin a shekarata 1982.To sai dai tsohon alkalin ya fada a zaman na yau cewa yan shia 148 da aka yankewa hukuncin kisa a wancan lokaci,sun amince da laifinsu a shariar data dauki kwanaki 16 tana gudana,kana yace babu kananan yara acikin wadanda aka kashen,kamar yadda aka fada.Amma ya amince dacewa dukkan mutane lauya guda daya aka basu domin karesu,wanda kuma kotunsa ce ta gabatar dashi ayayin zaman shariar na shekarata 1984.