Shari′ar ridda a Afghanistan | Siyasa | DW | 22.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari'ar ridda a Afghanistan

A kasar Afghanistan an gabatar da shari'a akan wani dan kasar da ya rugumi addinin Kirista

Maganar ta ridda da Abdurrahman yayi ta fito bainar jama’a ne ta kai ga mahukunta sakamakon sabani tare da iyalinsa a game da wanda zai dauki alhakin renon ‘ya’yansu guda biyu. A lokacin da ‘yan sanda suka kame shi a farkon watan fabarairun da ya wuce sai aka sami injila tare da shi. A gaban kotu Abdurrahaman ya hakikance cewar ya rungumi addinin kirista kuma yayi imanin da Annabi Isa AS. A farkon shekaru na 1990 wata kungiyar taimako ta kirista ta dauke shi aiki a kasar Pakistan domin kula da ‘yan gudun hijirar Afghanistan da suka bar kasarsu sakamakon yakin basasa. A wancan lokaci ne Abdurrahman ya rungumi kiristanci ya kuma yi zama na shekaru da dama a nan Jamus kafin ya tsayar da shawarar sake komawa gida a shekarar da ta wuce. A yanzun dai an gabatar da shari’a kansa a wata kotu dake birnin Kabul. Kwararrun masana sun nuna cewar wannan shari’ar ita ce ta farko irinta da aka gabatar a kasar ta Afghanistan tun bayan kifar da mulkin Taliban shekaru hudu da rabi da suka wuce. Mai daukaka kara da sunan gwamnati ya nemi da a yanke masa hukuncin kisa bisa tsarin shari’ar Musulunci dake haramta ridda ga musulmi. A karkashin daftarin tsarin mulkin Afghanistan dai dukkan ‘yan kasar na da ikon kama addinin da suke sha’awa, amma musulunci shi ne addinin da hukuma ta amince da shi kuma shi ne a’ala akan daftarin tsarin mulki. Ana dai sa ran cewar za a yi tsawon watanni biyu ana gudanar da shari’ar akan Abdurrahaman kuma kotun ta ce yana iya sake komawa ga addininsa na musulunci domin hana hukuncin kisa akansa. A kuma halin da ake ciki ministan tattalin arzikin kasar ta Afghanistan Amin Farhang yayi fatali da sukan da ake wa shari’ar, inda ya ce a hakika ya fahimci damuwar da ake yi a game da wannan batu, amma bai kamata a wuce gona da iri wajen yayata maganar ba. Ministan tattalin arzikin ya ce barazanar da Jamus tayi game da janye sojojinta daga Afghanistan tamkar wani mataki ne na neman ci da ceto. Shari’ar za a yi ta ne tsakani da Allah kuma da wuya a yanke masa hukuncin kisa. A dai misalin watanni biyu da suka wuce an gabatar da wata shari’a makamanciyar wannan wadda daga karshe aka saki mai laifin. A saboda haka ba wani abin haufi game da shari’ar ta Abdurrahaman.