Shari′ar Omar khadr a Guantanamo | Siyasa | DW | 10.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari'ar Omar khadr a Guantanamo

Ana gudanar da shari' ar wani ɗan kasar Canada mai suna Omar khadr a Guantanamo bisa zargin gudanar da ayyukan ta'addaci.

default

Zaman kotu a Guantanamo

Shi dai wannan ɗan ƙasar Canadan mai suna Omar Khadr, an kamashi ne a watan yuli ta shekara ta 2002 a kusa da ɗaya daga cikin sansanonin ƙungiyar Al-Qaida. Hukumomin na Amirka na zarginsa da tayar da gurneti da yayi sanidiyar rasa ran wani sojanta a lokacin da rundunar ƙasar ke fito na fito da 'yan taliban. Janar John Altenburg mai ritaya, da ya shugabancin kotun soja a lokacin da George W. Bush ke kan karagar mulki, ya na daga cikin waɗanda suka tattare da imanin cewa wannan matashin ya aikata wannan ɗanyen aikin:

" Akwai kwararun shaidu da ke nuna cewa shi ne ya jefa gurnetin da ta hallaka sojan na Amirka."

Sai dai lawyan da ke kare Omar khadr, wato leftenan-kanal Jon Jackson ya ce babu ƙamshin gaskiya a zargin da ake yi ma wannan matashi mai shekaru 23 da haihuwa.

"Shaidun da aka dogara akansu na nunawa a fili cewa omar Khadr ba harba wannan gurneti ba."

Guantanamo - Klagen gegen Verdächtige fallengelassen

Omar Khadr lokacin da ya ke da shekaru 16.

Lawyan Jackson ya nunar da cewa kamata yayi ayi la'akari da shekarun Omar da ba su fi 15 ba a lokacin da aka kamashi. Amma kuma bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa, ƙarancin shekarun ba zai hana a daureshi ba, idan aka sameshi da laifin da ke da dangantaka da ayyukan tarzoma ba.

Bayan darewarsa kan karaga, shugaba barck Obama na Amirka ya ci gaba da alƙawarin rufe sansanin ƙare kukanka na Guatanamo, tare da rusa kotunan soja da wanda ya Bush ya kafa. Duk da kurin da shugaban na Amirka ke yi cewa an rage musguna ma waɗanda ake tsare da su, amma gudanar na shari'ar na Omar na ci ma wasu amirkawa tuwo a kwarya, saboda ganin da suka yi cewa shugabansu yayi amai, ya lashe. Wani ɗan jaridan ƙasar ta Amirka wato Spencer Ackerman da ya saba bin diddigin hanrkokin da suka shafi shari'a ya ce da akwai alamun da ke nuna cewa ana matsa ma Omar khadr lamba.

" Mun jiyo cewa bayan da aka kama shi Omar Khadr, aka kuma tasa ƙeyarsa zuwa Baghram, yayi fama da cin mutunci a inda duk da rauni da yayi fama da shi, inda aka ɗaure masa hannaye da ankwa, aka Kuma sa ya ɗorasu a ka."

Kindersoldaten - Omar Khadr

Omar khadr a yanzu

Bayanan da aka tattaro daga Guantanamo sun nunar da cewa , a duk lokacin da ya rage kwana guda a yi ma Omar khadr tambayoyi, ana canza masa makwanci bayan awa uku-uku, domin hanasa barci. Lawyoyin shi Omar da aka haifa a Toronta na canada, sun sanya wani bangare da tambayoyin da jami'an tsaron ƙasarsa ta haihuwa suka yi masa a lokacin da ya ke da shekaru 16 a duniya.

Ita dai ƙasar Canada ba ta nemi Amirka ta mika mata Omar Khadr domin ta yi masa shari'a, kamar yadda yarjeniyar da ke tsakaninsu ta tanada ba. Amma fadar mulki ta Otawa ta ce da akwai bukatar gudanar da shari'ar cikin gaskiya da adalci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Zainab mohammed Abubakar