Shari′ar kisan gillan Marwa el-Sherbini a Dresden | Siyasa | DW | 26.10.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari'ar kisan gillan Marwa el-Sherbini a Dresden

Al'ummomin Masar na jiran suga yadda shari'ar kisan gillan

default

Marwa El Sherbiny

A yau ne aka fara sauraron shari'ar kisan gilla da wani Bajamushe haifaffen ƙasar Rasha yayi wa wata Balarabiya 'yar ƙasar Masar a gaban kotun birnin Dresden dake gabashin Tarayyar Jamus.

A ranar 1 ga watan Juli nedai Bajamushen Alex W. ya daɓawa Marwa El-Sherbini wuka dai-dai har sau 18 a gaban majinta da ɗanta mai shekaru 3 da haihuwa a gaban kotun birnin na Dresden, adaidai lokacin da take bada shaida akanshi.

Alex wanda a yanzu yake tsare a kurkuku, yana fuskanatar zargin kisan gilla da yunkurin kisan gillan maigidan Marwa wanda shima ya daɓawa wuka, ayayinda ake cigaba da gudanar da binciken kan lafiyar hankalinsa.

Alex dai yasha kiran Marigayiyar 'yar ta'adda A harabar kotun da akayiwa marigayiyar kisan gilla ne dai aka fara sauraron wannan shari'ar. An tsaurara matakan tsaro a haraba da kewayen kotun,da kimanin jami'an 'yansanda kimanin 200.

Marwa El Sherbiny

Marwan da Mijinta

Shari'ar dai na ɗaukar hankalin magabatan Jamus dana ƙasashen ketare, musamman al'ummar Masar waɗanda ke jiran su ga yadda zata kaya, tunda fatansu shine kashe duk wanda yayi kisan gilla. Duk dacewar a yanzu an samu lafawan lamura, ba kamar lokacin da aka kashe Marwa ba a watanh Yuli.

Taken cibibiyar raya al'adun Jamus dake birnin Alkahira ta Goethe dai shine, shine tattauna al'adun jamus. A gaban wannan cibiya dake tsakiyar birnin Alkahira kuwa tawagar 'yammata ne ke tsaye ,dukkan kawunansu ɗaure da ɗankwali, kamar yadda marigayiya Marwa el-Sherbini ta sabayi. Ko me ɗaliban ke fada dangane da shari'ar ta birnin Dresden...

" ina jiran a yanke mai hukuncin kisa. Ba tare da nuna banbanci ba. Ba tare da la'akari dacewar Bajamushe ne ya kashe balarabiya ba. Amma shari'ar adalci. Domin da zai iya zama balarabe ne ya kashe bajamushe"

" duk wanda yayi kisa to ya zamanto wajibi a kashe shi. Wannan itace shari'ar gaskiya. Amma a Jamus babu hukuncin kisa.Nasan cewar wannan itace matsalar. Dokokinsu ba kamar namu bane"

Marwa El-Sherbini

Jana'izar Marwa

"nasan za a cimma shari'ar data fi dacewa. Domin tabbatarwa da kasarmu dama duniya baki ɗaya adalci"

A yanzu haka dai babu kalamai na ɓacin rai a tsakanin al'ummar masar dangane da kisan gillan da akayi Marwa, idan aka kwatanta da lokacin da abun ya faru a watan Yuli.

Shugabar ƙungiyar kyautata dangantaka tsakanin Jamus da Masar Reda Sheta, tayi fatan cewar wannan mummunan abu daya faru ba zai ɓata kyakkyawar dangantakar ƙasashen biyu ba.

"Ta ce wannan abu ne da mutum guda ya aikata.Kuma dole ayi la'akari da haka. Jamus da Masar sunyi Allah wadan wannan abu. Tarzoma matsala ce da duniya ke fama da ita, kuma dole ne a maganta ta.Bashi da alaka da addini ko ƙasa"

Mijin marigayiya el-Sherbini da ɗan uwanta Tarek suna birnin Dresden domin sauraron shari'ar.Sai dai Mahaifin Marwa Ali el-Sherbini, har yanzu yana cikin bakin cikin rabuwa da 'yarsa..

"Yace idan da ace hakan ya kasance ne da 'yar Angela Merkel, da me zatayi? ko kuma wata uwa Bajamushiya?Menene matsalar ɗankwalin da Marwa take ɗaurawa?Mahaifiyyar Annabi Isa (A.S) ta daura kanta, kazalika Hadimai mata dake hidima a Coci, menene matsala idan mutun na rufe kanshi"

Da yawa daga cikin mutane musamman a nahiyar turai dau basu fahinci dalilan da yasa mata musulmi ke rufe kasuwansu ko kuma daura ɗankwa liba. A yayinda wasu kuwa ke masa kallon ra'ayi ne kawai na waɗanda suka zabi yin haka.

Mawallafiyya: Zainab Mohammed

Edita: Ahmad Tijani Lawal