1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar Charles Taylor na kokarin daukar sabon salo

March 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3Z

Hukumar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta yaba da matakin mika tsohon shugaban kaasar Liberia, izuwa hannun kotun kasa da kasa dake zaman ta a saliyo.

Hukumar ta Human rights Watch ta hannun daraktan ta mai kula da yammacin kasashen Africa, wato Richard Dicker, ta tabbatar da cewa matakin zai taimaka wajen ganin an hukunta tsohon shugaban dai dai gwargwadon laifin daya tafka lokacin mulkin sa.

A waje daya kuma rahotanni sun nunar da cewa tuni wannan kotu dake gudanar da zaman ta a saliyo ta yanke kudurin mika Charles Taylor izuwa kotun kasa da kasa dake birnin heg na kasar Holland, don sauraron kararrakin da ake tuhumar tsohon shugaban kasar ta Liberia.

Kotun ta kasa da kasar dake sauraron kararrakin wadanda suka aikata miyagun laifuffuka a kasar ta Saliyo tace ta dauki wannan matakin ne a sabili da dalilai na tsaro.

Kotun dai ta kasa da kasa na zargin Charles Taylor ne da gudanar da miyagun aiyuka a lokacin zamanin mulkin sa a kasar ta Liberia.

Rahotanni dai sun nunar da cewa jamian tsaro a Nigeria sun samu damar cafke Mr Charles Tylor ne a iyakar kasar da Kamaru, a yayin da yake kokarin tserewa, bayan ya shafe shekaru uku yana gudun hijira a kasar.