Sharia´ar Noriega a Faransa | Siyasa | DW | 27.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharia´ar Noriega a Faransa

Kotun Faransa ta gurfanar da tsofan shugaban ƙasar Panama Jana Manuel Noriega tare da zargin mallakar kuɗaɗen haram.

default

Kotun Faransa ta gurfanar da Janar Noriega

Yau ne kotunan ƙasar Faransa ta gurfanar da tsofan shugaban mulkin kama karyar na ƙasar Panama, Janar Manuel Noriega,da ake zargi ta lefin sarrafa kuɗin ganyi da kuma safara miyagun ƙwayoyin.

Daren Litinin ne zuwa sahiyar Talata, jami´an tsaro suka kawo Janar Manuel Noriega daga Amirka zuwa ƙasar Faransa, tare da amincewar gwamnatin Amirka.

Cemma dai Kotun Amirka ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 17 a kurkuku, bayan ta tabbatar da cewar yana safara miyagun ƙwayoyi.

Sannan tun shekara 1999 wata kotun France ta yanke masa hukunci shekaru goma a kurkuku, ba tare da halarci kotun ba.

Hukumomin Faransa na zargin Manuel Noriega da aje haramttatun kuɗaɗe da yawan su ya kai Euro miliyan biyu da kusan rabi, a cikin bankunan Faransa.

Paris ta buƙaci Amirka ta bada damar maido Noriega Faransa, inda zai fuskanci zargin da kotu keyi masa.

Saidai masu bin diddiƙin wannan shari´a na nuni da cewar wannan shari´a ce mai sarƙƙaƙƙiya, kamar yadda Harold Hyman wani ɗan asulin Amurika da ke Faransa, kuma masani game da harakokin  hulɗoɗin ƙasa da ƙasa ya yi bayyani:

A shekarun baya Manuel Noriega ya samu lambar ban girma daga shugaban kasar Faransa.Albarkacin wannan lambar, dole kotu tayi masa sassauci.Itama Amirka da farko ta na da alaƙar ƙut da ƙut da Noriega.

Kamin sojojin Amirka su hamɓare Janar Noriega daga karagar mulkin Panama, a shekara 1990, ya kasance mai ma´amila tare da cibiyar lerken asirin CIA.

To saidai Amirka ta ɗauki matakin sauke shi daga mulki a dalili da kusancinsa da shugaban ƙasar Kuba Fidel Castro da kuma Muhamar Ƙhadafi na Libiya.

A cewar Bernard Valero, kakakin ofishin ministan harakokin wajen ƙasar Faransa shari´ar Manuel Noriega ta cencenzi zuwa kotun ƙasa da ƙasa:

Shekaru da dama Noriega yayi zaman gidan kurkuku Faransa.Ya kamata ace kotunan ƙasa da ƙasa su gurfanar da shi a matsayin yaƙi da masu aikatan miyagun lefika.

Shi dai tsofan shugaban kasar Panama mai shekaru 76 a duniya,har yanzu  yana mussanta zargin da ake yi masa.

Mawwallafi: Husseina Jibrin Yakubu Edita: Yahouza Sadissou Madobi