Shari´a a Afghanistan | Labarai | DW | 03.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari´a a Afghanistan

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai, ya bukaci ƙasashen dunia su ci gaba da tallafawa ƙasar sa, duk da matsalolin da a ke fuskanta tare da mayaƙan Taliban.

Karzai ya yi wannan jawabi, albarkacin taron ƙasa da ƙasa da ke gudana a ƙasar Italia, a game da batun ingata harakokin shri´a a Afghanistan shekaru 6 bayan kifar da mulkin yan Taliban.

Karzai, ya yi hamdalla da ci gaban da Afghanistan ta samu ta fannin kare yancin bil adama, ta hanyar wanzuwar shari´a cikin adalci.

Saisdai ya tabatar da cewar har yanzu akwai sauran rina kaba,a a game da batunyaki da harakokin cin hanci, da karɓar rashawa, da su ka yi ƙwai su ka ƙyenƙyasa a kotunan Afghanistan.

Afghanistan na da jama´a milion 30, to saidai jimlar lauyoyin ƙasar, sun tashi 220, a sakamakon haka, a na fuskantar cinkosso, a game da harakokin shari´a, inji shugaba Hamid Karzai, wanda yayi kira ga ƙasashen masu hannu da shuni, su taimaka wajen girkuwar shari´a ta gari.