Shariár wasu muƙarabban Saddam a ƙasar Iraqi | Siyasa | DW | 21.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shariár wasu muƙarabban Saddam a ƙasar Iraqi

A cigaba da shariár manyan na hannun daman Saddam, kotun musamman a Iraqin zata saurari tuhumar kisan gillar da aka yiwa yan Shia a lokacin boren Intifada a shekarar 1991.

Tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussaini

Tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussaini

Yan shiá kimanin dubu ɗari ɗaya ne aka yi ƙiyasin an kashe a lokacin da sojojin Saddam suka yi musu dirar mikiya domin murƙushe boren da suka yi masa a wancan lokaci. Shariár ta yau ita ce ta uku da babbar kotun ta musaman da aka naɗa domin shariár munanan laifukan da tsohuwar gwamnatin ta aikata za ta yi hukunci a kan manyan jamián Saddam waɗanda suka haɗa da ɗan uwan sa Ali Hassan Majid wanda aka fi sani da suna Chemical Ali.

Tuni dama dai kotu ta yankewa Ali Hassan Majid wanda tsohon Ministan tsaro ne a zamanin Saddam hukuncin kisa a dangane da rawar da ya taka a kisan gillar da aka yiwa yan ƙabilar ƙurdawa marasa rinjaye a arewacin Iraqi a shekarar 1988. A kuma lokacin bore Intifada bayan da sojin taron dangi ƙarƙashin jagorancin Amurka suka fatattaki dakarun Saddam daga Kuwaiti a lokacin yaƙin tekun fasha, a sannan ne sojoji Saddam ɗin suka yi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu inda suka buɗe wuta ta kisan kan mai uwa da wabi ga yan shiár wanda ya hallaka mutane kusan dubu ɗari ɗaya.

Tsohon shugaban Iraqin Saddam Hussaini wanda aka hambarar da shi daga karagar mulki a mamayen sojin taron dangi a shekarar 2003, a ranar 30 ga watan Disamba na shekarar da ta wuce aka rataye shi sakamakon hukuncin da kotu ta yanke masa bayan samun sa da laifin kisan yan shiá 148 a ƙauyen Dujail.

A halin da ake ciki kuma shugabanin Iraqin da suka haɗa da shugaban ƙasar Jalala Talabani da P/M Nuri al-Maliki da manyan yan siyasar ƙasar na kurdawa da sunni da kuma shiá na shirin gudanar da taro domin shawo kan dambarwar siyasa da halin kakanika yi da ƙasar ta sami kan ta a ciki.

A ɓangare guda kuma, Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner wanda ya kai ziyara Iraqin a jiya ya gana da shugaban ƙasar jalalal Talabani da shugaban kurdawa Massoud Barzani. A jawabin sa Ministan harkokin wajen na Faransa yace ko da yake Faransa bata goyi bayan yaƙin ba tun da farko, akwai buƙatar a manta da baya a kuma duba yadda zaá taimakawa ƙasar domin ɗorewar zaman lafiya. Kouchner yace majalisar ɗinkin duniya na da gagaruwamar rawar da zata taka wajen samar da masalaha a tsakanin alúmomin Iraqin.

Rahotanni dai daga Iraqin na cewa an sako a ƙalla fursunoni fiye da ɗari ɗaya bayan bincike da wani kwamiti da P/M Nuri al-Maliki ya kafa ya gano cewa basu da laifi.

A wani cigaban kuma wasu gaggan sanatoci biyu na Amurka Carl Levin da kuma John Warner sun bada shawarar cewa kamata yayi majalisar dokokin Iraqi ta sauya gwamnatin Nuri al-Maliki idan ta kaucewa dama ta ƙarshe ta sasanta dambarwar siyasar ƙasar. A ƙoƙarin samun daidaituwar Iraqin, P/M Nuri al-Maliki a ya kai ziyara Syria dake maƙwabtaka da Iraqi domin samun goyon bayan ta ga ɗorewar zaman lafiya a ƙasar ta Iraqi.