Shariár Charles Tyalor a birnin Hague
March 31, 2006Kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya dake shariár laifukan yaki ta bukaci maida shariár tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor daga Saliyo zuwa birnin Hague a kasar Netherlands saboda matakan tsaro.
A ranar Larabar da ta gabata ce aka tasa keyar Charles Taylor sanye da ankwa a hannun sa zuwa kasar Saliyo domin amsa tuhuma a kan laifukan yaki. Charles Taylor zai kasance tsohon shugaba na farko a Afrika da zai gurfana a gaban kotun kasa da kasa. Babban mai shariár Justice A Raja N. Fernando ya baiyana fargabar cewa magoya bayan Charles Taylor na iya tada yamusti a lokacin zaman shariár. Maáikatar harkokin wajen kasar Netherland da kuma kotun ta kasa da kasa na nazarin bukatar domin bada sahalewa. A waje guda kuma shugabar kasar Liberia Ellen Johson Sirleaf ta baiyana cewa dangi da yan uwan Charles Taylor da kuma masu yi masa hidima wadanda har yanzu suke zaune a Nigeria na iya dawo wa gida ba tare da wata fargaba ba, domin ba zaá tuhume su da wani laifi ba.